Tikitin Musulmi Da Musulmi Kaddara Ce Daga Allah, Shugaban APC, Adamu

Tikitin Musulmi Da Musulmi Kaddara Ce Daga Allah, Shugaban APC, Adamu

  • Sanata Abdullahi Adamu, shugaban jam'iyyar APC na kasa ya ce zabin Asiwaju Bola Tinubu da Kashim Shettima a matsayin yan takarar shugaba da mataimaki a 2023 kaddara ce ta Allah
  • Shugaban na jam'iyyar ta APC mai mulki a kasa ya yi wannan furucin ne a Daura yana mai sanar da kiristocin Najeriya cewa zabin ba zai saka a tauye musu hakki ba
  • Tsohon gwamnan na Jihar Nasarawa ya ce Shettima cikakken dan Najeriya ne wanda halayensa ne suka saka aka zabe shi bayan tattancewa

Katsina - Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, a ranar Laraba, ya bawa kiristoci tabbacin cewa babu abin tsoro game da tikitin musulmi da musulmi na Sanata Kashim Shettima da Asiwaju Tinubu a zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan

Mun daina bacci har sai Tinubu da Shettima sun gaje Buhari, Matasan APC a arewa

Tinubu, Adamu da Shettima
Tikitin Musulmi Da Musulmi Kaddara Ce Daga Allah, Shugaban APC, Adamu. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

Ya ce zabin musulmi da musulmi na jam'iyyar a zaben shugaban kasar "kaddara ce ta Allah."

Adamu ya yi wannan jawabin ne a Daura lokacin da ya jagoranci Kwamitin Ayyuka na Jam'iyyar yayin ziyarar Sallah da suka kaiwa Shugaba Muhammadu Buhari, rahoton The Punch.

Ya kuma shaidawa manema labarai a Daura cewa shi da tawagarsa sun yi wa shugaban kasa bayanin abin da ya faru wurin yakin neman zabe na gwamna a Osun na APC.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mun yi tuntuba sosai kafin zaben Shettima, Adamu

Adamu ya yi bayanin cewa sunyi tuntubar da ta dace yayin zaben dan takarar da mataimakinsa.

Ya bayyana Shettima a matsayin dan Najeriya wanda bai bukatar zama musulmi ko kirista kafin a zaben shi don matsayin da ya cancanta.

Adamu ya nuna godiya ga kiristocin Najeriya don nuna sha'awarsu kan tikitin musulmi da musulmi.

Kara karanta wannan

Ba za mu sake yiwa Tinubu kamfen ba saboda zabar Musulmi da ya yi, Kiristocin APC a arewa

Ya kara da cewa:

"APC na aiki tare da addu'ar ganin ta ci babban zabe da ke tafe a 2023. Kuma munyi imanin lashe zaben gwamnan Osun da ke tafe a ranar Asabar."

Martanin Gwamna Masari kan zabin Shettima

Gwamna Aminu Masari na Jihar Katsina shima ya yi martani kan zabin Shettima a matsayin abokin takarar Tinubu ya bayyana shi a matsayin hazikin mutum mai basira da hakuri wanda ke da duk halayen da ake bukata a mataimakin shugaban kasa.

Masari ya ce yana goyon bayan zabin Shettima dari bisa dari.

Tinubu: Abin Da Yasa Na Zabi Musulmi A Matsayin Abokin Takara Na A 2023

A wani rahoton, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), a zaben 2023 ya kare zabinsa na Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin takara, Daily Trust.

Kafin bayyana Shettima a matsayin mataimaki, siyasar kasar ta dauki zafi kan batun zaben yan takara masu addini iri daya.

Kara karanta wannan

2023: Na sanyawa Tinubu da Shettima albarka, in ji Ali Modu Sheriff

Yayin da kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, ta yi gargadin hakan, wasu masu ruwa da tsaki sun bukaci yan Najeriya su mayar da hankali kan cancanta fiye da addini ko kabila.

Asali: Legit.ng

Online view pixel