2023: Tinubu ya ci zabe ya gama, In ji tsohon dan takarar kujerar gwamna a Plateau

2023: Tinubu ya ci zabe ya gama, In ji tsohon dan takarar kujerar gwamna a Plateau

  • Tsohon dan takarar gwamnan jihar Plateau a APC, David Victor Dimka, ya bayyana cewa Bola Ahmed Tinubu ne zai lashe zaben shugaban kasa na 2023
  • Dimka ya ce Tinubu na da abubuwan da ake bukata daga shugaba duba ga tarin nasarorin da ya samu a lokacin da yake matsayin gwamnan jihar Lagas
  • Dan siyasar ya kuma ja hankalin yan Najeriya da su duba cancanta a zaben ba wai tikitin Musulmi da Musulmi ba

Plateau - Tsohon dan takarar gwamnan jihar Plateau karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), David Victor Dimka, ya yi hasashen cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Ahmed Tinubu ne zai lashe zaben 2023.

Dimka, wanda ya kasance tsohon kwanturolan hukumar kwastam a wata hira da manema labarai a garin Jos, ya ce Tinubu dan siyasa ne da ya yarda da hadin kai da ci gaban Najeriya a matsayin kasa daya, Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tikitin Musulmi Da Musulmi Kaddara Ce Daga Allah, Shugaban APC, Adamu

Ya bayyana cewa duba ga tarin nasarorinsa a siyasa, Tinubu mutum ne wanda ke da abun da ake bukata don inganta Najeriya, duba da irin ci gaban da ya samu wanda a cewarsa ya shafi dukkan bangarorin rayuwa a fadin kasar.

Bola Tinubu
2023: Tinubu ya ci zabe ya gama, In ji tsohon dan takarar kujerar gwamna a Plateau Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Idan aka zo kan batun buga siyasa, yana da abun da ake bukata don sauya lamura saboda kwarewarsa a harkar siyasa, wayewa da kuma sanin mutane da ya yi a fadin duniya.”

Kan zabar Musulmi da Tinubu ya yi a matsayin abokin takararsa, Dimka ya yarda da abu guda cewa:

“Idan kana da shugaba toh ka dunga duba zuwa gare shi da tatson sa ba wai abokin takararsa ba saboda daukar mataimaka ake yi ba zaben su ba.”

Ya kuma jaddada cewa siyasa wasa ce ta lambobi, kuma abu guda ya da ya kamata a yi la’akari da shi shine aminci da nagartan abokin takarar da ya zaba.

Kara karanta wannan

Mun daina bacci har sai Tinubu da Shettima sun gaje Buhari, Matasan APC a arewa

Dimka ya bukaci yan Najeriya da su duba nasarorin da Tinubu ya samu yayin da yake matsayin gwamnan Lagas da kuma yadda ya hada hannu da kungiyoyin damokradiyya a kasar don kawo damokradiyya a Najeriya a 1999 wajen zabarsa a 2023, rahoton Daily Independent.

Tikitin Musulmi Da Musulmi Kaddara Ce Daga Allah, Shugaban APC, Adamu

A gefe guda, shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, a ranar Laraba, ya bawa kiristoci tabbacin cewa babu abin tsoro game da tikitin musulmi da musulmi na Sanata Kashim Shettima da Asiwaju Tinubu a zaben shugaban kasa na 2023.

Ya ce zabin musulmi da musulmi na jam'iyyar a zaben shugaban kasar "kaddara ce ta Allah."

Adamu ya yi wannan jawabin ne a Daura lokacin da ya jagoranci Kwamitin Ayyuka na Jam'iyyar yayin ziyarar Sallah da suka kaiwa Shugaba Muhammadu Buhari, rahoton The Punch.

Asali: Legit.ng

Online view pixel