Kalaman nan ya sa miliyoyi ke fama da talauci – Obi ya yi wa Kwankwaso raddi

Kalaman nan ya sa miliyoyi ke fama da talauci – Obi ya yi wa Kwankwaso raddi

  • Peter Obi ya maida martani ga Rabiu Musa Kwankwaso wanda aka yi tunanin zai hada-kai da shi
  • Obi ya yi tir da kalaman Kwankwaso na cewa mutanen yankin Arewa ba za su zabi LP a 2023 ba
  • ‘Dan takarar shugaban kasar na LP ya ce siyasar kabilanci ya jefa kasar nan a irin halin da ta ke ciki

Abuja - ‘Dan takarar shugaban Najeriya a karkashin jam’iyyar LP, Peter Obi ya samu damar tanka Rabiu Musa Kwankwaso mai neman mulki a NNPP.

A wata hira da aka yi da Peter Obi a gidan talabijin na Arise TV, an yi masa magana a game da kalaman da aka ji daga bakin Rabiu Musa Kwankwaso.

Kwankwaso ya fito yana cewa mutanen Arewa ba za su zabi Peter Obi, don haka ya neme shi da su hada-kai tare a zaben 2023 domin doke APC da PDP.

Kara karanta wannan

Kungiyar IPOB sun ja-kunnen Kwankwaso, sun ce ya daina hada su da Peter Obi

Da Peter Obi yake maida martani, The Nation ta rahoto shi yana cewa irin kalaman da suka fito daga bakin Rabiu Kwankwaso ya sa ake fama da talauci.

Me Peter Obi ya fada?

“Maganar da babban yayana Kwankwaso ya yi, shi ne dalilin da muke da mutum miliyan 100 da ke zama a talauci, yara miliyan 18 ba su zuwa makaranta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kusan 52% na mutanen kasar nan ba su aiki, ko ba su da aiki mai tsoka. Maimakon zaben shugabannin da suka dace, sai a biyewa kabilanci da addini.
Peter Obi
'Dan takaran LP, Peter Obi
Asali: Twitter

“A yau ba za ka iya tafiya daga Abuja zuwa Kaduna ta titi ko jirgin kasa. Shin saboda mutumin Kudu maso gabas yana mulki ne? Ba za ka iya zuwa Minna ta titi ba….
A jiya (Ranar Talata), mun samu ‘yan bindiga sun kai wa ayarin motocin shugaban kasa hari a Katsina. Saboda 'Dan Kudu maso gabas yana muki ne?"

Kara karanta wannan

Ya kamata ka girmi siyasar kabilanci: Peter Obi ya caccaki Kwankwaso

- Peter Obi

Kowa yana cikin Ni 'Ya su - Obi

Premium Times da ta bibiyi hirar, ta ce Obi ya kulabalanci mutane su nuna masa inda ake sayen kayan abinci da araha saboda mutumin Arewa yana mulki.

A amsar da ya bada, ‘dan takaran na LP ya yi kira ga mutane da su fuskanci matsalolin kasar nan, su guji nuna kabilanci ko sabanin addini wajen zabe.

An ji ‘dan siyasar yana cewa komai ya tabarbare a halin yanzu, don haka yake bukatar mutane su zabe shi domin kawo gyara, ba la’akari da yankin da ya fito ba.

IPOB ta dura kan Kwankwaso

A baya mu na da labari Kungiyar Indigenous People of Biafra wanda mutane suka fi sani da IPOB sun ce da su da Peter Obi, hanyar jirgi dabam, na mota dabam.

Mai magana da yawun IPOB ya yi raddi ga Rabiu Kwankwaso bayan wasu kalamansa da aka ji. IPOB ta ce ba ta da alaka da Obi, kuma babu ruwanta da siyasa.

Kara karanta wannan

Okupe: Abin da ya sa tun tuni Peter Obi ya yi watsi da maganar dunkulewa da Kwankwaso

Asali: Legit.ng

Online view pixel