Kungiyar IPOB sun ja-kunnen Kwankwaso, sun ce ya daina hada su da Peter Obi

Kungiyar IPOB sun ja-kunnen Kwankwaso, sun ce ya daina hada su da Peter Obi

  • ‘Yan Kungiyar Indigenous People of Biafra sun maidawa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso raddi
  • Kakakin IPOB ya nesanta kan su daga Peter Obi, ya ce ba su da wani hadi da ‘dan takaran na LP
  • IPOB ta fadawa Rabiu Kwankwaso cewa babu ruwanta da batun mulki, burinta kafa kasar Biyafara

Kungiyar Indigenous People of Biafra wanda aka fi sani da IPOB, ta gargadi Rabiu Musa Kwankwaso cewa ya daina danganta ta da Peter Obi.

Jaridar PM News ta fitar da rahoto a makon nan, inda aka ji kungiyar ta IPOB ta na cewa babu abin da ya hada gwagwarmayar da take yi da Peter Obi.

A wani jawabi da Mai magana da yawun bakin IPOB ya fitar, Emma Powerful ya tabbatar da babu abin da ya hada kungiyarsu da wani sha’anin zabe.

Kara karanta wannan

Ya kamata ka girmi siyasar kabilanci: Peter Obi ya caccaki Kwankwaso

Powerful yake cewa ‘dan takaran shugaban kasar na jam’iyyar LP watau Peter Obi, bai taba goyon bayan yunkurin su na raba Najeriya da Biyafara ba.

Jawabin Kakakin IPOB

“Mutanen kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB), a karkashin jagorancin shugabanmu, Mazi Nnamdi Kanu, mu na so mu yi kira ga Rabiu Kwankwaso.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ka da tsohon gwamnan na Kano ya jefa IPOB a cikin batun kiran a gudanar da zabe a Najeriya.
Kwankwaso
Hamisu Mailantarki da Rabiu Kwankwaso a Gombe @SaifullahiHon
Asali: Twitter
Gaba daya ‘Yan siyasar Najeriya da musamman Kwankwaso su guji alakanta neman takarar shugaban kasar Peter Obi da ‘Yan IPOB. Obi ba ‘dan IPOB ba ne.
Bai taba goyon bayan kiran mu na neman ‘yanci ba domin wani burin ya sa a gaba, wanda ya sha ban-bam a na IPOB. Ba mu sha’awar tsarin siyasar Najeriya."

- Emma Powerful

Kwankwaso ya hangi barazana

Kara karanta wannan

Okupe: Abin da ya sa tun tuni Peter Obi ya yi watsi da maganar dunkulewa da Kwankwaso

Daily Post ta rahoto Powerful yana cewa ‘dan takaran na NNPP ya daina yunkurin hada su da Obi saboda ganin irin goyon bayan da ‘dan takaran LP yake samu.

A jawabin na ta, kungiyar nan ta caccaki Kwankwaso, ta zarge shi da boye manufarsa na kin yadda ya yi wa Obi takarar mataimaki saboda tsabagen son mulki.

A je a dawo, IPOB ta ce tana kan bakarta na ganin mutanen Kudu maso gabas sun bar Najeriya.

Tinubu a tsaka mai wuya

Za a ji labari an kai karar Bola Tinubu a kotu, ana neman hana shi canza abokin takarar wucin gadin da ya ba hukumar INEC sunansa domin zaben 2023.

Wasu wanda suke zaben ‘dan takara a jam'iyyar APC da sun ce idan aka taba sunan Kabiru Ibrahim Masari, to an lalata tikitin APC a zabe mai zuwa da za ayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel