Zaben gwamnan Osun: Buhari ya karbi bakuncin Oyetola, ya ce APC ce za ta lashe zaben

Zaben gwamnan Osun: Buhari ya karbi bakuncin Oyetola, ya ce APC ce za ta lashe zaben

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Adegboyega Oyetola, dan takarar APC a zaben gwamnan Osun
  • Buhari ya kuma gabatar masa da tutar jam’iyyar mai mulki a wani dan taro da aka gudanar a yau Laraba, 6 ga watan Yuli
  • Shugaban kasar ya nuna karfin gwiwar cewa jam’iyyarsa za ta lashe zaben da za a yi kwanan nan cikin gaskiya da adalci

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Osun - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna karfin gwiwar cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) za ta yi nasara a zaben gwamnan jihar Osun mai zuwa cikin gaskiya da adalci.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 6 ga watan Yuli, lokacin da ya mika tutar jam’iyyar ga dan takarar APC, Gwamna Adegboyega Oyetola, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Dan takarar gwamna a Kaduna ya hada kai da 'yan Shi'a don nemawa Peter Obi kuri'u

Buhari ya mika tutar APC ga dan takarar gwamnan Osun
Zaben gwamnan Osun: Buhari ya karbi bakuncin Oyetola, ya ce APC ce za ta lashe zaben Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Buhari wanda ya bayar da tabbacin cewa jam’iyyar ta himmatu wajen ciyar da jihar gaba, ya yaba da kokarin Gwamna Oyetola na yiwa al’ummarsa hidima a wa’adin mulkinsa na farko, Channels Tv ta rahoto.

Shugaban kasar ya kuma jinjinawa jagororin kwamitin yakin neman zaben gwamnan jihar Osun, Gwamna Babajide Sanwo Olu da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, da kuma mataimakin shugaban kwamitin, Gwamna Abubakar Sani Bello kan himma da suka sa wajen kamfen don ganin an sake zabar Gwamna Oyetola.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu ya nakalto ubangidan nasa na cewa:

“Ina yi maka fatan alkhairi.”

Da yake martani game da gayyatarsa zuwa babban gangamin karshe da za a yi a mako mai zuwa, shugaban kasar ya ce:

“Ina fatan zan hallara don zaburar da kai.”

Mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Abba Kyari, wanda ya gabatar da dan takarar a madadin Sanata Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyyar na kasa, ya yabama shugaban kasar kan jagorantar jam’iyyar zuwa ga nasara.

Kara karanta wannan

Kungiyar da ta sayawa Tinubu Fom din N100m, ta ce Elrufai take goyon bayan ya zama mataimaki

Ya bayyana Oyetola a matsayin gwamna mai aiki wanda ya yi namijin kokari a wa’adinsa na farko kuma ya cancanci wa’adi na biyu.

Ya kuma nuna yakinin cewa jam’iyyar ce za ta yi nasara a babban zaben kasar mai zuwa.

Peter Obi: A madadin kwararru, 'yan tasha ne ke tafiyar da lamurran kasar nan

A wani labari na daban, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ya ce yan tasha ne ke jan ragamar harkokin Najeriya maimakon a samu kwararrun masu lasisi.

Obi ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 6 ga watan Yuli yayin da ya bayyana a shirin safiya na Arise TV.

Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya kara da cewar abubuwan farko da yan Najeriya ke dubawa a yayin zabe shine ya jefa kasar a halin da take ciki a yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel