Kungiyar da ta sayawa Tinubu Fom din N100m, ta ce Elrufai take goyon bayan ya zama mataimaki

Kungiyar da ta sayawa Tinubu Fom din N100m, ta ce Elrufai take goyon bayan ya zama mataimaki

  • Kungiyar TSO ta bayyana goyon bayan ta ga mallam Elrufai da ya zama abokin takarar Tinubu a zabe mai zuwa
  • Elrufai gogaggen dan siyasa ne da ya fi kowa cancanta ya zama maiataimakin Tinubu inji shugaban kungiyar TSO
  • Majiyoyi a jam'iyyar APC sun nuna cewa hankalin jam'iyyar ya karkata akan daukan Gwamna zullum ko senata Shettima a matsayin mataumakin Tinubu

Jihar Kaduna : Gabanin wa'adin ranar 17 ga watan Yuli da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ba wa jam'iyyun siyasa su mika sunayen 'yan takararsu a zaben 2023, kungiyar TSO ta amince da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya zama mataimakin dan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu, kamar yadda ChannelsTV ta rwaito.

Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa ne a jam’iyyar APC mai mulki, ya fito fili ya ce har yanzu yana neman abokin takararsa.

Kara karanta wannan

Mance da su Ganduje da El-Rufai: Ka zabi abokin takara da Arewa ta tsakiya, jiga-jigan APC ga Tinubu

Majiyoyi a jam’iyya APC sun nuna cewa daya cikin gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum da tsohon gwamnan jihar, Sanata Kashim Shettima aka fi so Tinubu ya dauka matsayin mataimakin sa.

Amma da yake zantawa a wani taron manema labarai a ranar Litinin a Kaduna, Darakta-Janar na TSO, Aminu Suleiman, ya ce kungiyar ta zabi El-Rufai ne bayan ganawa da masu ruwa da tsaki daga shiyyar arewa maso yamma da sauran su.

ELRUF
TSO sun goyi bayan Elrufai ya zama mataimakin BolaTinubu Foto Channel TV.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya yi imanin cewa zabar abokin takarar na da matukar muhimmanci ga nasarar Tinubu a 2023, don haka kungiyar ta tantance duk wani zabin da za ta yi na son dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC ya fito daga yankin Arewa maso Yamma, wanda shi ne mai mafi yawan kuri’u a kasar.

Kungiyar ta kara da cewa, Elrufai gogagge ne fagen siyasa da mulki a matakin tarayya da jiha kuma shi ne dan takarar da ya dace da Tinubu a matsayin mataimakin shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Kungiyar Afenifere tayi kira ga jiga-jigan yan siyasan Yarabawa su marawa Tinubu baya

"Bayan tuntubar juna da masu ruwa da tsaki musamman a yankin Arewa maso Yamma, tabbas El-Rufai ya kamata yayi wa Asiwaju mataimaki," in ji Suleiman.
“Kungiyar TSO tana aiki tuƙuru don ganin an zaɓi Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban ƙasar Najeriya. TSO ta yi imanin cewa zabar abokin takara shine muhimmin abun da zai kawo nasara Asiwaju.

Babu yankin da zai iya samar da shugaban kasa shi kadai, inji kungiyar Afenifere

Jihar Ekiti : Kungiyar Afenifere ta bukaci ‘yan siyasa daga yankin Kudu maso Yamma da su hada kai da sauran shiyyoyi biyar na kasar domin tabbatar da aniyar tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu, na zama shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa ya yiwu. rahoton PUNCH

Sakataren Yada Labarai na Afenifere, Michael Ogungbemi, ya yabawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kungiyar gwamnonin APC, yan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC da suka janye wa Tinubu da ‘ya’yan jam’iyyar da suka yi ruwa da tsaki dan ganin ya samu damar tsayawa takarar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel