Peter Obi: A madadin kwararru, 'yan tasha ne ke tafiyar da lamurran kasar nan

Peter Obi: A madadin kwararru, 'yan tasha ne ke tafiyar da lamurran kasar nan

  • Peter Obi ya daura alhakin halin da ake ciki yanzu a Najeriya kan abubuwan da yan Najeriya suka fi ba fifiko a yayin zabe
  • Obi ya bayyana cewa ana daukar yan tasha domin su jagoranci al’amurran kasar nan maimakon a yo hayar kwararru
  • Dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar Labour Party ya yi kira ga al’ummar Najeriya da su zabi wanda ya cancanta a 2023 don samun mafita

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ya ce yan tasha ne ke jan ragamar harkokin Najeriya maimakon a samu kwararrun masu lasisi.

Obi ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 6 ga watan Yuli yayin da ya bayyana a shirin safiya na Arise TV.

Peter Obi
Peter Obi: A madadin kwararru, 'yan tasha ne ke tafiyar da lamurran kasar nan
Asali: UGC

Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya kara da cewar abubuwan farko da yan Najeriya ke dubawa a yayin zabe shine ya jefa kasar a halin da take ciki a yanzu.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Bana son tsohon hannu ya zama mataimakina, na fi son matashi mai jini a jika, Peter Obi

Dan takarar shugaban kasar ya ja hankalin yan Najeriya da su tabbata sun zabi dan takarar da ya cancanta a 2023 domin jan ragamar al’amuran kasar, rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

“Yan Najeriya na yawan daukar hayar yan tasha maimakon daukar hayar kwararru don jagorantar kasar.”

Shugaban kasa a 2023: Bana son tsohon hannu ya zama mataimakina, na fi son matashi mai jini a jika, Peter Obi

A gefe guda, mun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, a ranar Laraba, 6 ga watan Yuli, ya magantu a kan wanda yake so ya zama abokin takararsa a babban zaben 2023 mai zuwa.

Obi ya bayyana cewa idan son samu ne, ya fi kaunar matashi mai jini a jika ya zamo masa dan takarar mataimakin shugaban kasa, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Mutane da dama sun jikkata yayin da yan daba suka farmaki taron PDP a Kogi

Ya kara da cewar ya fi son matashi wanda ke da abubuwan gabatarwa da za su tallafawa tikitinsa maimakon sake dauko tsoffin hannu wadanda suke dade a gwamnati.

Asali: Legit.ng

Online view pixel