Jerin mutum 11: Buhari ya yiwa majalisar ministocinsa garambawul

Jerin mutum 11: Buhari ya yiwa majalisar ministocinsa garambawul

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yiwa majalisar ministocinsa garambawul bayan amincewa da wadanda ya nada
  • Shugaban ya kuma rantsar da mutum bakwai da ya zaba domin maye gurbin ministocinsa da suka yi murabus
  • A baya dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi takardun ajiye aiki na wasu ministocinsa da suka nufi tsayawa takara a zaben 2023

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa majalisar ministocinsa garambawul da sabbin ministoci da aka ba shi mukamai.

TheCable ta fahimci cewa mukaman ministoci 11 ne hakan ya shafa a wannan sabon garambawul da ya zo gabanin babban zaben 2023.

Buhari ya yi sabbin nade-nade
Yanzu-Yanzu: Buhari ya zabi Mu'azu Sambo ya zama ministan sufuri na Najeriya | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ga jerin garambawul din Buhari:

  1. Adeleke Mamora - ministan kimiyya da fasaha (tsohon karamin ministan lafiya)
  2. Mu’azu Jaji Sambo - ministan sufuri (tsohon ministan wutar lantarki)
  3. Umanna Okon Umanna - ministan harkokin Neja Delta
  4. Sharon Ikeazor - karamin ministan Neja Delta (tsohon karamin ministan muhalli)
  5. Gbemisola Saraki - karamar ministar ma’adinai da karafa (tsohuwar karamin ministan sufuri)
  6. Umar Ibrahim EI-Yakub - minista, ayyuka da gidaje
  7. Goodluck Nanah Opiah - karamin ministan ilimi
  8. Ekumankama Joseph Nkama - karamin ministan lafiya
  9. Ikoh Henry Ikechukwu - karamin ministan kimiyya da fasaha
  10. Odum Udi - karamin ministan muhalli
  11. Ademola Adewole Adegoroye - karamin ministan sufuri

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro ya sa masarautar Katsina ta dakatar da hawan Sallah

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakazalika ministoci bakwai da majalisar dattawa ta tabbatar da nadin su a ranar 29 ga watan Yuni shugaban kasa ya rantsar da su a gaban taron majalisar zartarwa ta tarayya, kamar yadda PM News ta ruwaito.

Ministocin sun hada da: Umanna, El-Yakub, Opiah, Nkama, Udi, Adegoroye da kuma Ikechukwu.

An nada su ne domin cike gurbin da Rotimi Amaechi, Ogbonnaya Onu da wasu biyar da suka yi murabus a watan Mayu domin cimma burin siyasa.

Nadin sabbin ministoci: Na so Buhari ya dawo da Amaechi bisa dililai, Shehu Sani

A wani labarin, tsohon sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya ce ya so ace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake zabar Rotimi Amaechi a matsayin ministan sufuri.

Daily Trust ta rahoto cewa Sani ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 21 ga watan Yuni, a yayin hira da gidan talbijin na Channels.

Kara karanta wannan

Saboda tsaro: Kungiya ta gargadi APC da Tinubu kan tikitin Musulmi da Musulmi

Buhari dai ya aika da sunayen mutane bakwai zuwa majalisar dattawa domin a maye gurbinsu da ministocin da suka yi murabus don neman mukaman siyasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel