Rashin tsaro: Sarkin Katsina ya dakatar da Hawan Sallar Idi

Rashin tsaro: Sarkin Katsina ya dakatar da Hawan Sallar Idi

  • Masarautar Katsina ta sanar da dakatar da hawan Daushe a lokacin bikin Idi saboda matsalar tsaro da jihar ke fuskanta
  • Sarki Katsina Abdulmumini Kabir Usman ya shawarci al'umma musulmi su rika yiwa jihar adu'o'i da kasar baki daya

Jihar Katsina - Masarautar Katsina ta sanar da dakatar da hawan Daushe a lokacin bikin sallar Eid-el-Kabir da za a gudanar a ranar Asabar. Rahoton Daily Nigeria

Dakatawar ta fito ne a jawabin da mataimakin sakataren majalisar masarautar jiha, Sule Mamman-Dee ya fitar a ranar Talata.

Ya ce an dakatar da bikin ne saboda matsalar tsaro da ake fama da shi a jihar.

A cewar Mamman-Dee, Sarki, Abdulmumini Kabir-Usman, ya nuna matukar damuwarsa kan matsalar tsaro a sassan masarautar inda ya ce zai halarci Sallar Idi ne kawai a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: Hotuna sun nuna lokacin da Tinubu ke matashi, ya halarci jami'a a Turai

emire
Rashin tsaro: Sarkin Katsina ya dakatar da Hauwan Sallar Idi; FOTO : Daily Nigeria
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya bayyana cewa Sarkin ya shawarci al’ummar Musulmi da su ci gaba da yin addu’o’in samun zaman lafiya a jihar da kasa baki daya.

Bikin Durbar dai ya samo asali ne tun shekaru aru aru, kuma ya kunshi baje kolin fasahar hawan doki daga gundumomi da masu fada aji, wadanda ke nuna girmamawa ga Sarkin a ranar Idi da aka fi sani da ‘Hawan Daushe’.

A nasa bangaren, Sarkin ya bukaci tawagar ‘yan majalisar Masarautu da Hakimai cikin jerin gwanon dawaki da aka fi sani da ‘Hawan Bariki’ su je su yi mubaya’a ga Gwamnan Jihar, kwana guda bayan kammala Idi.

Adadin wadanda aka kashe a Shiroro ya kai 48, ciki akwai Soji 34: Inji shugaban matasan yankin

A wani labari, Rahotanni da ke fitowa na nuna cewa an gano karin gawarwakin sojoji da jami’an ‘yan sanda da aka kashe a wani harin kwantan bauna da ‘yan ta’adda suka kai garin Shiroro na jihar Neja rahoton jaridar VANGUARD.

Sani Kokki, shugaban matasan na jihar Neja, ya bayyana haka a ranar Lahadi, inda yace adadin wadanda suka mutu ya kai 48.

Asali: Legit.ng

Online view pixel