Peter Obi ya sake jan-kunnen magoya baya, ya nuna masu hanyar farauto zuciyar mutane

Peter Obi ya sake jan-kunnen magoya baya, ya nuna masu hanyar farauto zuciyar mutane

  • Peter Obi ya yi kira da babban murya ga magoya bayansa da su rika bin masu adawa da shi a hankali
  • ‘Dan takaran shugaban Najeriyan ya ce ana bukatar girmama ra’ayin kowa domin gamsar da mutane
  • Masu kiran kan su OBidient a shafukan sada zumunta ba su saurarawa duk wanda ya saba masu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Lagos - Peter Obi wanda yake neman takarar zama shugaban Najeriya a jam’iyyar Labour Party (LP), ya yi kira ga duk wadanda suke goyon bayansa.

Peter Obi ya fito shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, 3 ga watan Yuli 2022, ya na fadawa masu goyon bayansa su rika girmama ra’ayin sauran jama’a.

‘Dan takaran ya yi wannan magana ne ganin wadanda suke tare da shi, suke yi wa duk wanda ya sabawa gwanin su rubdugu a shafukan sada zumunta.

Kara karanta wannan

Rabiu Kwankwaso bai cire ran hada-kai da Peter Obi ba, duk da 'Yan hana ruwa gudu

Poju Oyemade v OBidient

The Cable ta ce Obi ya bada wannan sanarwa ne biyo bayan abin da ya faru tsakanin mutanensa da Poju Oyemade na cocin Covenant Christian Centre.

Kwanakin baya Fasto Oyemade ya yi kira ga matasa da su daina biyewa Obi domin za su yi asarar kuri’arsu ne, nan ta ke magoya baya su ka dura kan sa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake bayani a shafinsa da kimanin karfe 2:30 na jiya, Obi ya yabi masu goyon bayan ya zama shugaban kasa, amma ya ce akwai bukatar su canza salo.

Peter Obi
'Dan takaran LP, Peter Obi Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Maganar da Peter Obi ya yi

“Ina mai godewa magoya bayana na yin imani da ni da kuma niyyata na samar da Najeriyar da za a samu hadin-kai, tsaro, kasa ta tafi daidai.”
“Amma, ina sake yin kira da cewa mu rika girmama ra’ayin sauran mutane, wadanda suka saba, da kuma wadanda suka ci karo da na mu.”

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Amaechi ya fada ma magoya bayansa wanda za su zaba

- Peter Obi

A cewar Obi, watakila za ma a iya daukar darasi daga cikin ra’ayin wadanda suka saba masu.

“Duk da za a iya fahimtar abin da ya jawo fushin da ake ji, dole mu yi amfani da karfinmu ta hanyar da za ta amfanar domin shawo kan wasu.”
“Ko da cewa sakon mu yana cigaba da yaduwa da samun karbuwa a nesa, amma akwai wadanda sai an yi aiki sosai wajen iya gamsar da su.”
“Dole mu yi wannan sannu a hankali, domin gudun mu rufe kofar hada-kai da wasu mutanen a nan gaba, wajen ganin mun gyara kasa.”

- Peter Obi

LP ba za ta ci zabe ba - Kwankwaso

An ji labari Mai neman zama shugaban kasa a NNPP, Rabiu Kwankwaso ya ce babu yadda za ayi mutanen yanki daya su iya ba mutum shugabancin kasar nan.

Rabiu Kwankwaso yana ganin LP ba ta shahara a wajen yankin Kudu maso gabas ba, kuma doka ta ce sai ‘dan takara ya samu karbuwa a ko ina a fadin Najeriya.

Kara karanta wannan

Al-Mustapha: A Shirye Na Ke In Mutu Domin 'Yan Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel