Al-Mustapha: A Shirye Na Ke In Mutu Domin 'Yan Najeriya

Al-Mustapha: A Shirye Na Ke In Mutu Domin 'Yan Najeriya

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Action Alliance a zaben 2023, Hamza Al-Mustapha ya ce a shirye ya ke ya mutu don Najeriya da yan Najeriya
  • Tsohon dogarin marigayi Janar Sani Abacha ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels Television
  • Al-Mustapha ya ce fatarsa shine ya zama shugaban Najeriya kuma ya amsa kirar ne saboda magoya bayansa daga kudu da arewa sun matsa ya fito

Hamza Al-Mustapha, tsohon hadimin marigayi Janar Sani Abacha ya jadada kudirinsa na zama shugaban kasar Najeriya a shekarar 2023.

Hamza Al Mustapha
Al-Mustapha: A Shirye Na Ke In Mutu Domin 'Yan Najeriya. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

Al-Mustapha, wanda shine dan takarar shugaban jam'iyyar Action Alliance, AA, a zaben 2023 ya ce a shirye ya ke "ya sadaukar da rayuwarsa don Najeriya da walwalar yan Najeriya".

Kara karanta wannan

Wike Ya Saki Hoto Da Magana Mai Boyayyen Ma'ana Bayan Jita-Jitar Ganawarsa Da Tinubu a Faransa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya yi wannan jawabin ne a ranar Juma'a yayin hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels Television.

"Wannan karon na amsa kiran yan Najeriya da dama, manya da yara daga Arewa zuwa Kudu da kungiyoyi da dama. Kiran ya zo ne daf da lokacin mika fom din takara ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta.
"Mun zauna kun kalli wasu jam'iyyun, mun zabi wanda akidunmu suka zo daya muka gano Action Alliance na da abin da muke bukata. Mun shiga Action Alliance kuma muna ta aiki ta karkashin kasa tun bayan gangamin taro. Muna aiki tukuru," wani sashi cikin jawabinsa.

Al-Mustapha ya ce fatansa shine ya zama shugaban Najeriya kuma ayyukan da ya yi a baya sun isa zama hujja a kansa.

"Na yi aiki a wurare da dama kafin in zama soja. Na yi abin da ba za ka iya fahimta ba cikin gaggawa, musamman yi wa Najeriya hidima. Abin da muka yi a soja hujja ne."

Kara karanta wannan

Bincike ya nuna dukiyar Attajirai 2 za ta iya fito da mutum miliyan 63 daga talauci

Zaben 2023: Ba Zan Yi Wa INEC Katsalandan Ba, In Ji Buhari

A bangare guda, Shugaba Muhammadu Buhari ya sake jadada cewa gwamnatinsa za ta tabbatar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC, ta yi zabe na adalci kuma cikin zaman lafiya a 2023.

Ya bada tabbacin cewa ba zai yi wa INEC katsalandan ba, yana mai cewa bayan kammala zaben cikin gida na jam'iyyu, yanzu an sa ido ne kan zaben 2023 a Najeriya.

Buhari, a cewar sanarwar da kakakinsa Garba Shehu ya fitar a shafinsa na Twitter, ya yi magana ne a daren ranar Laraba a Lisbon yayin ganawarsa da yan Najeriya da ke zaune a Portugal.

Asali: Legit.ng

Online view pixel