A Karshe, Lawan Ya Karanto Wasikar Shekarau Ta Sauya Sheka Zuwa NNPP Mai Kayan Marmari

A Karshe, Lawan Ya Karanto Wasikar Shekarau Ta Sauya Sheka Zuwa NNPP Mai Kayan Marmari

  • Sanata Ahmad Lawan, Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya ya karanto wasikar sauya sheka ta Sanata Ibrahim Shekarau daga APC zuwa NNPP
  • Tun da dai cikin watan Mayu ne tsohon gwamnan na Jihar Kano ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar mai mulki ta kasa zuwa NNPP mai kayan marmari
  • Shekarau, cikin wasikar ya bayyana cewa rashin adalci, wariyya na rashin demokradiyyar cikin gida da wasu dalilan yasa ya fice daga APCn

FCT Abuja - A Karshe, Majalisa ta karanto wasikar sauya shekar da tsohon gwamnan Kano kuma sanata mai wakiltar Kano Central, Ibrahim Shekarau, The Punch ta rahoto.

Shugaban majalisa, Ahmad Lawan ne ya sanar da sauya shekarsa yayin da majalisar ta fara zamanta na yau.

Sanata Ibrahim Shekarau.
A Karshe, Lawan Ya Karanto Wasikar Shekarau Ta Sauya Sheka Zuwa NNPP Mai Kayan Marmari. Hoto: @daily_nigerian.
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Zawarcin Kwankwaso Ya Koma APC: NNPP Ta Yi Wa Jam'iyyar APC Kaca-Kaca

Shekarau ya fice daga APC ya koma NNPP a watan Mayu amma sai yau Laraba aka karanto wasikar sauya shekarsa.

Tuni dai sanatan ya karbi katinsa na NNPP a mazabarsa ta Giginiyu a gaban manyan yan siyasa irin su Dr Rabiu Kwankwaso da tsohon dan majalisa, Suleiman Sumaila.

Kamar saura, shekarau a wasikarsa ta murabus, ya ambaci rashin adalci, wariyya da gwamnan Kano Abdullahi Ganduje a matsayin dalilinsa na barin jam'iyyar.

Wasikar ta ce:

"Na rubuta don sanar da kai a hukumance ficewa ta daga jam'iyyar All Progressives Congress, da komawa New Nigerian People’s Party.
"Na yi murabus daga APC ne saboda wariya daga manyan masu ruwa da tsaki, da rashin demokradiyya ta cikin gida, a APC ta Kano, da rashin dama wa da ni a harkokin jam'iyya da gwamnati a jihar.
"Bayan tuntuba da masu irin tunani na da magoya baya na a jihar, mun yanke shawarar fita daga APC zuwa NNPP.

Kara karanta wannan

Cikakken jerin Sanatoci 58 da aka zazzage, ba za su koma kujerunsu a Majalisar Dattawa ba

"Ina maka fatan alheri tare da cigaba da bada hadin kai a koda yaushe."

Bayan karanto wasikar, Shugaban majalisar ya umurci bulaliyar majalisa ya yi wa Shekarau rakiya zuwa bangaren da yan hammaya ke zama.

Shekarau Ya Fita Daga APC, Ya Koma NNPP Ya Haɗe Da Kwankwaso

Tunda farko, kun ji cewa Sanata Ibrahim Shekarau, mai wakiltar Kano ta Tsakiya ya fita daga jam'iyyar APC mai mulki a kasa ya koma NNPP mai kayan marmari, rahoton aminiyya.

Tsohon gwamnan na Kano ya fice ne karkashin jagorancin tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso, jigo na kasa a jam'iyyar ta NNPP.

Yakubu Yareema, wani na hannun daman Malam Shekarau ya sanar da hakan a yammacin ranar Talata kamar yadda Freedom Radio ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel