Cikakken jerin Sanatoci 58 da aka zazzage, ba za su koma kujerunsu a Majalisar Dattawa ba

Cikakken jerin Sanatoci 58 da aka zazzage, ba za su koma kujerunsu a Majalisar Dattawa ba

  • Sanatoci akalla 58 ne aka tabbatar da cewa ba za su koma Majalisar Dattawa bayan zaben 2023 ba
  • Watakila wannan sauyi da za a samu ya shafi shugaban Majalisar kasar nan, Dr. Ahmad Lawan
  • Ike Ekweremadu wanda ya dade yana kan kujerar mataimakin shugaban majalisa ba zai zarce ba

Abuja - Rahoton da Premium Times a ranar 28 ga watan Yuni 2022 ya nuna cewa ba za a ga fuskar akalla Sanatoci 58 a zauren majalisar dattawa a 2023 ba.

Dalilai da-dama su ka jawo wannan zazzaga kamar dai yadda aka saba gani a siyasar kasar nan. Masana na ganin yawan sababbin shiga yana kawo cikas a kasa.

A kan dauki lokaci (har shekaru biyu) kafin ‘dan majalisa ya fahimci aikinsa, don haka yawan canza Sanatoci da ‘yan majalisa bayan 'yan shekaru ke jawo ci-baya.

Kara karanta wannan

Amimu ya shaki iskar 'yanci: Yadda aka mika matashin ga iyayensa daga magarkama

Haka zalika kuma wasu ‘yan majalisar na amfani da wannan dama, su dade ba tare da wani tasiri ba. A 2023, za a zubar da kusan 50% na Sanotocin da ake da su a yau.

Me ya jawo haka?

1. Rigima da Gwamnoni

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daga cikin dalilan da aka bada a rahoton na rasa kwararrun Sanatoci shi ne rigimar da aka saba tsakanin ‘Yan majalisa da kuma Gwmanonin jihohinsu.

Irin haka ya sa aka hana Ibrahim Shekarau, Abdullahi Yahaya, Adamu Aliero, da Babba Kaita tikiti. Sai dai wasu daga cikinsu sun koma wata jam’iyyar.

2. Kwadayin zama shugaban kasa

Wasu Sanatocin sun raba hankalinsu, a wajen kwadayin zama shugaban kasa, suka rasa tikitin Sanata. Misali Ahmad Lawan wanda yake rikici da Bashir Machina.

A wannan sahun akwai Sanatocin Ogun, Imo da Ondo da suka yi biyu-babu. Ibikunle Amosun Ajayi Boroffice da Rochas Okorocha ba su zarce a zaben 2023 ba.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Uwargidan Shugaban Kasa ta Huce, Ta Janye Karar Dalibin da ya ‘Zageta’

3. Takarar Gwamna

Wasu Sanatocin za su bar majalisa saboda neman zama Gwamna a Delta, Taraba da Kaduna. A nan akwai Ovie Omo-Agege, Emmanuel Bwacha da Uba Sani

Haka zalika akwai Aishatu Dahiru, Teslim Folarin da Sandy Onor da za su nemi Gwamna a 2023 a tunanin AnHalliru Dauda Jika zai yi takarar Gwamna a NNPP.

Sanatoci
'Yan Majalisar Dattawa Hoto: @NgrSenate / Tope Brown
Asali: Twitter

4. Tsarin karba-karba

A wasu jihohi a kan yi yawo da kujerar Sanata tsakanin mazabu domin a tafi da kowane yanki. Wannan na cikin abin da ya jawo wasu Sanatocin ba za su koma ba.

5. Hakura da takara

Irinsu Remi Tinubu sun zabi su hakura da majalisa ne bayan sun yi shekaru. Sanata Nora Daduut da Theodore Orji ba su zarce ba, sun zabi su bar wa wasu kujerar.

6. Samun wani mukamin

Sanata Abdullahi Adamu da Abba Kyari sun ajiye aikin majalisa ne bayan zamansu shugabannin APC. Hassan Mohammed kuma ya zama mataimakin gwamna.

Kara karanta wannan

Kame dalibi kan zagin matar Buhari: Dalibai sun fadi matakin da za su dauka kan Aisha Buhari

Jerin ragowar Sanatocin da za su bar majalisa a 2023:

  1. Dimka Hezekiah
  2. Gyang Istifanus
  3. Smart Adeyemi
  4. Yakubu Oseni
  5. Sabi Abdullahi
  6. Godiya Akwashiki
  7. Ibrahim Oloriegbe
  8. Orker-Jev Emmanuel
  9. Yusuf Yusuf
  10. Amos Bulus
  11. Ayo Akinyelure
  12. Nicholas Tofowomo
  13. Tolu Odebiyi
  14. Matthew Urhoghide
  15. Gershom Bassey
  16. James Manager
  17. George Sekibo
  18. Betty Apiafi
  19. Albert Bassey
  20. Chris Ekpenyong.
  21. Rochas Okorocha
  22. Hadejia Ibrahim
  23. Sankara Abubakar
  24. Mohammed Nakudu
  25. Bello Mandiya
  26. Barkiya Kabir
  27. Lawali Anka
  28. Danjumah La’ah
  29. Victor Umeh
  30. Moses Cleopas
  31. Mohammed Bulkachuwa
  32. Chukwuka Utazi

Asali: Legit.ng

Online view pixel