Da Ɗumi-Ɗumi: Shekarau Ya Fita Daga APC, Ya Koma NNPP Ya Haɗe Da Kwankwaso

Da Ɗumi-Ɗumi: Shekarau Ya Fita Daga APC, Ya Koma NNPP Ya Haɗe Da Kwankwaso

  • Daga karshe, Sanata Ibrahim Shekarau ya fice daga jam'iyyar All progressives Congress, APC, ya koma NNPP mai kayan marmari
  • Shekarau ya koma NNPP ne karkashin jagorancin tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso wanda shine jagoran jam'iyyar ta NNPP na kasa.
  • A baya-bayan nan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ziyarci gidan Ibrahim Shekarau da nufin shawo kansa don kada ya fice daga APC amma hakan bai yi wu ba

Jihar Kano - Sanata Ibrahim Shekarau, mai wakiltar Kano ta Tsakiya ya fita daga jam'iyyar APC mai mulki a kasa ya koma NNPP mai kayan marmari, rahoton aminiyya.

Tsohon gwamnan na Kano ya fice ne karkashin jagorancin tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso, jigo na kasa a jam'iyyar ta NNPP.

Da Ɗumi-Ɗumi: Shekarau Ya Fita Daga APC, Ya Koma NNPP Ya Haɗe Da Kwankwaso
Shekarau Ya Fita Daga APC, Ya Koma NNPP Ya Haɗe Da Kwankwaso. Hoto: NNPP Worldwide Platform.
Asali: Twitter

Yakubu Yareema, wani na hannun daman Malam Shekarau ya sanar da hakan a yammacin ranar Talata kamar yadda Freedom Radio ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ganduje ya kira zaman gaggawa a sakamakon rikicin da ke neman kunnowa APC a Kano

Ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Bayan wata ganawa an bayar da umurnin kowa ya bayar da shawara don haka daga baya muka cimma matsayar ficewa daga jam'iyyar APC zuwa NNPP don haka mu yanzu ba mu tare da APC."

Hakan na zuwa ne a yayin da ake fuskantar babban zabe na shekarar 2023 a Najeriya.

Dama cikin yan kwanakin nan an yi ta gana wa tsakanin Shekarau da Kwankwaso inda magoya baya ke ta fatan ganin Shekarau ya koma NNPP.

A baya-bayan nan Gwamna Ganduje ya ziyarci Shekarau a gidansa domin gayyatarsa zuwa Abuja yin wata zaman sulhu amma Shekarau bai tafi ba.

Mataimakin Kakakin Majalisar Kano Ya Fice Daga APC, Ya Bi Kwankwaso Jam'iyyar NNPP

A wani rahoton, mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Zubairu Hamza Massu, ya fice daga jam'iyyar All Progressives Congress, APC ya koma New Nigeria People's Party, NNPP, rahoton Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Dirama a Kano yayin da tawagar Kwankwaso ta dira gidan Shekarau awanni bayan tafiyar Ganduje

Mr Massu, ɗan siyasa daga mazabar Kano ta Kudu, ya sanar da ficewarsa daga APC cikin wata wasika da ya aike wa shugaban jam'iyyar na APC a mazabar Massu.

Ɗan majalisar ya bayyana rikice-rikicen jam'iyyar da rashin demokradiyya ta cikin gida a matsayin dalilin ficewarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel