Zawarcin Kwankwaso Ya Koma APC: NNPP Ta Yi Wa Jam'iyyar APC Kaca-Kaca

Zawarcin Kwankwaso Ya Koma APC: NNPP Ta Yi Wa Jam'iyyar APC Kaca-Kaca

  • Jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ta yi jam'iyyar APC gargadi ta dena zawarcin dan takarar shugaban kasarta Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
  • Shugaban NNPP na kasa Farfesa Alkali Ahmed Rufai Alkali ne ya yi wannan gargadin yana mai cewa rashin sanin halin da Najeriya ke ciki yasa APC ta yi wannan tayin
  • Farfesa Rufai ya ce tuni yan Najeriya sun fara gajiya da rashin iya tafiyar da gwamnati na APC kuma suna neman zabi kuma sun zabi NNPP a halin yanzu

FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar New Nigeria People Party (NNPP) na kasa, Prof. Alkali Ahmed Rufai Alkali, a jiya, ya kushe jam'iyyar All Progressives Congress (APC) saboda zawarcin dan takarar shugaban kasar ta, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya dawo cikinta.

NNPP da APC.
Zawarcin Kwankwaso Ya Koma APC: NNPP Ta Yi Wa Jam'iyyar APC Kaca-Kaca. Hoto: @LeadershipNGA.
Asali: Twitter

Alkali ya yi tir da kalaman da aka danganta ga mataimakin sakataren jam'iyyar APC na kasa Yakubu Ajaka na kira ga Sanata Rabiu Kwankwaso ya dawo APC saboda zai fi samun daman zama shugaban kasa a karkashin inuwarta.

Sai dai, Alkali cikin sanawar da ya ratabba wa hannu a jiya a Abuja ya ce wannan tunanin ya yi kama da na mutum da ke nutsewa kuma ya ke neman tallafi, Leadership ta rahoto.

Ya ce idan Ajaka zai iya nazarin yadda kasar ta ke a yanzu da ya gano yadda mambobin APC ke ficewa suna dawowa NNPP har ma da yan wasu jam'iyyun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kada a yi mamakin ganin Ajaka ya lallabo zuwa NNPP, in ji Alkali

A cewar Alkali, "Ba zan yi mamaki ba idan Ajaka ya kwankwasa kofar mu cikin yan kwanakin nan masu zuwa ya ce mu ba shi masauki."

Ya bayyana cewa yan Najeriya sun fara nuna rashin gamsuwarsu da APC don haka suna neman wani zabin mai nagarta kuma sun samu NNPP.

Ya kara da cewa jigon na APC yana rayuwa ne a zamanin baya kuma ya kamata a farka a tunkari abin da ke faruwa a yanzu.

Sanatan APC Ya Saka Wa Daliget Da Kujerun Hajji Bayan Sun Dawo Masa Da Kudinsa Don Ba Su Zabe Shi Ba

A wani rahoton, Sanata Smart Adeyemi wanda ya wakilci Kogi West a Majalisar Tarayya, ya bada kujerun Hajji ga mutum biyar cikin daligets din da ya bawa kudi amma ba su zabe shi ba a zaben fidda gwani na APC.

Adeyemi ya rasa damar komawa majalisar ne a yayin da ya samu kuri'u 43 a zaben fidda gwanin, hakan yasa ya zo na uku.

Sunday Karimi, wanda ya samu tikitin jam'iyyar ya samu kuri'u 288, yayin da Muyiwa Aina wanda ya zo na biyu ya samu kuri'u 73.

Asali: Legit.ng

Online view pixel