Jam’iyyar APC ta na marmarin Kwankwaso ya dawo, ta ce zai iya rike Najeriya nan gaba

Jam’iyyar APC ta na marmarin Kwankwaso ya dawo, ta ce zai iya rike Najeriya nan gaba

  • Yakubu Ajaka yana ganin ba zai yiwu Rabiu Musa Kwankwaso ya karbi mulki ba sai ya dawo APC
  • Mataimakin sakataren yada labarai na APC yana burin Rabiu Musa Kwankwaso ya fice daga NNPP
  • Ajaka yake cewa Kwankwaso da Peter Obi ba za su je ko ina ba da zarar an fara yakin zabe da kyau

FCT, Abuja - Mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyyar APC na kasa, Yakubu Ajaka ya yi kira ga Rabiu Musa Kwankwaso ya dawo APC da ya bari.

A wata hira da aka yi da Yakubu Ajaka, ya nuna cewa a halin yanzu Rabiu Musa Kwankwaso ba zai iya lashe zabe ba. Vanguard ta fitar da wannan rahoto.

Ajaka ya shaidawa manema labarai a garin Abuja cewa ba zai yiwu NNPP ta karbi shugabancin kasa ba, don haka zai yi kyau Kwankwaso ya sake tunani.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike ya fadi dalilin da ya sa 'Dan takaran NNPP, Kwankwaso ya ziyarce shi a gida

A cewar mataimakin kakakin na APC mai mulki, tsohon gwamnan na jihar Kano ya taka rawar gani sosai wajen nasarar da jam’iyyar ta samu a zaben 2015.

Ina ma ya dawo APC

Daily Nigerian ta rahoto Ajaka yana mai cewa jagororin jam’iyyar APC sun yi niyyar yi wa Kwankwaso sakayyar irin abin da ya yi masu a wancan lokaci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai sakataren yada labaran na APC ya ce ba zai yiwu a taimakawa Sanata Kwankwaso a yanzu da ya sauya-sheka zuwa wata jam’iyyar hamayya ba.

Kwankwaso
Kwankwaso da Wike Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

Ba a zama shugaban kasa a NNPP

“Shiyasa na ce bai makara da dawowa APC ba. Asali da nan ya fi dacewa, kuma yana da tabbacin zama shugaban kasa wata rana, ba kamar NNPP dinsa da ta yi suna a wani bangare kurum ba.”

Kara karanta wannan

Majan LP da NNPP: Sai dai Peter ya zama mataimaki, Kwankwaso shugaba, inji NNPP

“Ko da yake wasu mutane su na yaudararsa, har su na kiran shi Shugaban kasa, amma mutum ba zai iya karbar shugabancin Najeriya daga kuri’un jiha daya ko biyu a Arewa maso yamma ba.”
“Kwankwaso yana bukatar jam’iyyar da ta ratsa kasa irin APC domin ya cin ma burinsa na yin mulki. Saboda haka ina kiran shi da ya yi abin da ya kamata, tun kafin lokaci ya kure masa.”

- Yakubu Ajaka

Makomar Peter Obi da Atiku

Da aka tambayi Ajaka a game da Peter Obi, sai ya nuna cewa idan an buga gangar siyasa, mutane za su gane bambancin APC da jam’iyyar adawa irin Labor Party.

Ajaka yana ganin ana zuga tsohon gwamnan na Anambra ne a kafofin sada zumunta na zamani.

A game da Atiku Abubakar kuwa, Ajaka yake cewa APC ta saba doke PDP, don haka iyakar Atiku ya zo na biyu, ma’ana Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne zai ci zabe.

Kara karanta wannan

An sake samun Gwamnan APC da ya yi wa Tinubu alkawarin kuri’un Jiharsa a zaben 2023

An yi zama da Wike

A jiya aka ji cewa bayan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da tawagarsa sun koma gida daga Fatakwal, ‘Dan takaran ya yi magana a Twitter bayan kwanaki 20.

Mutanen Wike sun yi wa Kwankwaso kyakkyawar tarba a jihar Ribas, bayan an gama kus-kus, an ga Ayo Fayose yana yi wa jagoran NNPP ban-kwana a filin jirgi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel