Sanatan APC Ya Saka Wa Daliget Da Kujerun Hajji Bayan Sun Dawo Masa Da Kudinsa Don Ba Su Zabe Shi Ba

Sanatan APC Ya Saka Wa Daliget Da Kujerun Hajji Bayan Sun Dawo Masa Da Kudinsa Don Ba Su Zabe Shi Ba

  • Sanata Smart Adeyemi wanda ya wakilci Kogi ta Yamma a majalisa ya ba wa daliget 5 kujeran hajji saboda gaskiya da amana
  • Daliget din na Kogi su biyar kuma musulmi sun dawo wa Adeyemi da kudinsa na suka ce haramun ne gare su tunda ba su zabe shi ba don an hana su
  • Wannan abin ya sa Adeyemi ya ce ya basu kudin kyauta kuma ya musu alkawarin kujerun hajji a shekarar 2023 yana mai cewa sun sa ya kara girmama addinin musulunci

Sanata Smart Adeyemi wanda ya wakilci Kogi West a Majalisar Tarayya, ya bada kujerun Hajji ga mutum biyar cikin daligets din da ya bawa kudi amma ba su zabe shi ba a zaben fidda gwani na APC.

Kara karanta wannan

Matata Ta Roke Ni In Raba Wa Daligets Kudi, In JI Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam'iyyar ADC, Kachikwu

Adeyemi ya rasa damar komawa majalisar ne a yayin da ya samu kuri'u 43 a zaben fidda gwanin, hakan yasa ya zo na uku.

Sanata Smart Adeyemi
Sanatan APC Ya Saka Wa Daligets Da Kujerun Makka Bayan Sun Dawo Masa Da Kudinsa Don Ba Su Zabe Shi Ba. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Sunday Karimi, wanda ya samu tikitin jam'iyyar ya samu kuri'u 288, yayin da Muyiwa Aina wanda ya zo na biyu ya samu kuri'u 73.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da ya ke magana da yan jarida a Majalisar Tarayya a Abuja kan sakamakon zaben fidda gwanin da aka yi a ranar 28 na Mayun 2022, Adeyemi ya ce zaben tamkar 'fyyade' aka yi wa demokradiyya, fashi da makami a fili kuma an tafka magudi, rahoton Daily Trust.

Ya ce gwamna jiharsa ya sa shugaban jam'iyya ya kira taron sirri, aka nemi ya janye amma ya ki.

Adeyemi ya yi zargin cewa an tursasa wa daligets din su zabi abin da ba shi zuciyarsu ke so ba illa kalilan cikinsu.

Kara karanta wannan

Dan takarar shugaban kasa: Mata ta ta so na jika deliget da kudi, na ki, kuma na ci zabe

Ya ce biyar cikin daligets din daga karamar hukumar Koton Karfe sun dawo masa da kudin da ya basu na 'wurin kwana, cin abinci, da kudin mota' bayan ba su zabe shi ba.

Adeyemi ya musu tayin kujerar hajji

Adeyemi ya bada bayani dalla-dalla kan yadda daliget suka dawo masa da kudinsa saboda tsoron Allah

Dan majalisar ya ce ya ji dadin gaskiya da amana da suka nuna hakan yasa ya ce su rike kudin ya kuma yi alkawarin zai biya musu kudin kujerar hajji a 2023.

Ya ce:

"Dama mu kan bada wani tallafi ga daligets su kara kan kudin cin abinci, kudin mota da kudin otel da za su kwana. Amma, kada ku tambaye ni ko nawa ne.
"Daligets daga wata karamar hukumar, da musulmi suka fi yawa, ba a bari sun zabe ni ba saboda baturen zaben, wanda shima daga karamar hukumar ya ke kuma musulmi, ya fada musu su zabi Sunday Karimi, wanda ya fito daga mazabar da ke makwabtaka da nawa.

Kara karanta wannan

Kiyayya Ta Makantar Da Kai: Femi Adesina Ya Caccaki Oyedepo Kan Alkanta Gwamnatin Buhari Da Rashawa

"Sunan karamar hukumar Koton Karfe. Sati daya bayan zabe, su biyar sun zo Abuja kuma dukkansu musulmi ne. Sun fada min cewa haramun ne a musulunci ta karbi abin da ba naka bane.
"Don haka, sanata, kudin da ka bamu na kudin mota, abinci da wurin kwana, mun dawo maka da shi saboda ba a bari mun zabe ka ba. Amma kai ne dan takarar mu. Suka fashe da kuka, cewa an hana su zaben wanda suke so. Amma, don Allah ka dauki hoton mu don shaida da gaba.
"Ga kudinka. Na kalle su na ce kun saka na kara son musulunci a zuciyata duk da ni kirista ne. Kun dawo min da kudi na? Don Allah ku tafi da kudin. Na baku. Sai suka fara kuka kuma na basu tabbacin cewa shekara mai zuwa, ku biyar, zan biya muku kudin zuwa Makkah. Idan haka addinin ku na musulunci ya ke, toh, kun saka na kara girmama islama.

Kara karanta wannan

2023: Hadimin Ganduje Ya Bayyana Dalilan da Suka sa Ya Dace Ya Zama Mataimakin Tinubu

"Na biya wa akalla mutum 400 musulmi kudin zuwa Hajji. Amma mutum biyar musulmi su dawo min da kudin da na basu su ce haram ne. Abin ya sosa min zuciya.
"Ban taba sanin muna da irin wannan mutanen a Najeriya har yanzu ba. Sun dawo min da kudi na sun ce an hana su zabe na. Na dauki hotunan su."

Hatsaniya a Hedkwatar APC Yayin Da Masu Zanga-Zanga Ke Yi Wa Adamu Barazana

A wani rahoton, kun ji cewa hatsaniya ta barke a hedkwatar jam'iyyar APC na kasa da ke Abuja, a yayin da wasu gungun matasa suka shigo harabar jam'iyyar suna wakokin nuna kiyayya ga shugaban jam'iyyar na kasa Sanata Abdullahi Adamu.

Daily Trust ta rahoto cewa an ce matasan daga Jihar Kogi suke suka kutsa hedkwatar jam'iyyar yayin da ake taron kwamitin ayyuka na jam'iyyar, NWC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel