Ekiti: Na Yi Nadamar Shiga Siyasa, Ba Zan Sake Takara Ba, In JI Dan Takarar Gwamna na ADC

Ekiti: Na Yi Nadamar Shiga Siyasa, Ba Zan Sake Takara Ba, In JI Dan Takarar Gwamna na ADC

  • Wole Oluyede, dan takarar gwamna a zaben Ekiti karkakshin jam'iyyar ADC, a zaben ranar Asabar da ta gabata ya ce ya yi nadamar shiga siyasa da yin takarar
  • Oluyede ya yi ikirarin cewa mutanen Jihar na Ekiti sun gwammace su zabi wanda zai siya kuri'unsu a maimakon wanda zai warware musu matsalolin da ke addabarsu
  • Dan takarar, wanda likita ne mazaunin Australia ya ce ya koyi darasi kuma ba zai tafi kotu ba domin a cewarsa masu siyan kuri'un sun siya jami'an tsaro da ma'aikatan zabe don haka ba zai bata lokacinsa ba

Ekiti - Dan takarar gwamna na Jam'iyyar African Democratic Congress a zaben ranar Asabar na gwamna a Jihar Ekiti, Wole Oluyede, a ranar Laraba ya bayyana nadamar shiga siyasa, bayan rashin nasara da ya yi a zabe, rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Yobe North: Abin Da Yasa Muka Tura Wa INEC Sunan Ahmad Lawan, Shugaban APC, Adamu

Tambarin Jam'iyyar ADC
Ekiti: Na Yi Nadamar Shiga Siyasa, Ba Zan Sake Takara, Dan Takarar Gwamna na ADC. Hoto: @MobilePunch.

Oluyede, likita mazaunin Australia, wanda ya ce ya cire tsammani kan harkar zabe a Jihar Ekiti, ya ce, "Ba zan sake takara ba domin wanda ya fi kudi ne ke nasara don haka ba zan sake bata lokaci da karfi na ba."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan takarar na ADC, wanda ya zo na hudu a zaben, ya ce da gangan ya ki cire kudi ya siya kuri'a a zaben na ranar Asabar, ya kara da cewa, "na cire rai cewa wani abu zai gyaru a harkar zaben Ekiti, abin bakin ciki ne. Da gangan na ki siyan kuri'un mutanen Ekiti.
"Ba zan iya amfani da kudi na in zaga ina yi wa mutane magana kan dalilin da yasa za su zabe ni kuma duk da haka in cire kudi in siya kuri'arsu, jami'an tsaro da hukumar INEC. Bisa alamu dai ba wanda ya fi cancanta ke cin zabe ba," in ji shi.

Kara karanta wannan

Nasarar APC a Zaben Ekiti Babbar Alama Ce Ta Nasarori Masu Zuwa, Sanata Adamu

Ba zan tafi kotu ba - Oluyede

Oluyede ya kuma ce ba zai kallubalanci sakamakon zaben a kotu ba, yana mai cewa hakan zai zama bata lokaci ne kawai duba da ya yi ikirarin cewa dukkan harkar zaben babu gaskiya a ciki har da jami'an tsaro da hukumar zabe suna aljihun masu siyan kuri'ar ne.

Ya kara da cewa abin damuwa ne ganin cewa jama'ar jihar ba su son a warware musu matsalar talauci da suke fama da shi, don ya zo musu da mafita amma suna tsammanin ya siya kuri'unsu kafin su zabe shi ya taimake su. Ya ce wanda ya ci zaben ba shi ne ya fi cancanta ba amma shi ya dace da mutanen.

"Da amincewarsu ne. Babu wanda zai ce an tilasta musu karbar kudin. Na koyi sabuwar darasi a Ekiti. Da na sani, da ban zama dan siyasa ba, ballantana in yi takarar zabe," in ji shi.

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa 10 da Ya Dace a Sani Game da Zaben Gwamnan Ekiti

Ekiti 2022: 'Idan Ba Kuri'a, Ba Kudi', Bidiyon Tinubu Yana Yi Wa Masu Zabe Ba'a a Wurin Kamfen

A wani rahoton, Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a zaben 2023, Asiwaju Bola Tinubu, ya bukaci al'ummar Jihar Ekiti su fito su yi zabe idan ba hakan ba ba za a biya su ba.

Tinubu, wanda ya ziyarci a Jihar Ekiti a ranar Talata ya furta hakan ne wurin yakin neman zabe na dan takarar gwamna na jam'iyyar, Biodun Oyebanji gabanin zaben da ake shirin yi ranar Asabar 18 ga watan Yunin 2022.

Ya kuma kambama kansa cewa bai taba fadi zabe ba a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel