Nasarar APC a Zaben Ekiti Babbar Alama Ce Ta Nasarori Masu Zuwa, Sanata Adamu

Nasarar APC a Zaben Ekiti Babbar Alama Ce Ta Nasarori Masu Zuwa, Sanata Adamu

  • Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya kwatanta nasarar da aka samu a zaben Ekiti da alamar nasarar zabuka masu zuwa
  • Adamu, wanda ya bayyana jin dadinsa dangane da yadda Oyebanji ya tabbatar zababben gwamnan Ekiti, ya ce hikimar shugaban Buhari ce ta kawo nasarar
  • Ya mika godiyarsa ga shugaban kamfen din APC na zaben Ekiti, Atiku Bagudu, jama'ar jihar da kwamitin ayyuka kan yadda suka jajirce

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jam'iyyar APC mai mulki ta kwatanta nasarar da ta samu a zaben gwamnan jihar Ekiti da aka yi a ranar Asabar da ta gabata da alamar nasarar da take fata a zabukan gaba masu zuwa a fadin kasar nan.

Shugaban jam'iyyar na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana hakan a wasikar taya murna da ya aike wa zababben gwamna, Abiodun Oyebanji.

Shugaban jam'iyyar APC Na Kasa, Sanata Adamu Abdullahi
Nasarar APC a Zaben Ekiti Babbar Alama Ce Ta Nasarori Masu Zuwa, Sanata Adamu. Hoto daga @vanguardngrnews
Asali: Twitter

Mai bada shawara na musamman a harkar yada labarai ga shugaban APC na kasa, Muhammad Nata'ala Keffi, a wata takardar ya bayyana Sanata Adamu yana cewa, nasarar sakamakon ficen da 'dan takara Oyebanji yayi ne tare da karfafan tsarikan kamfen din da APC ta yi.

Kasantuwarsa zaben farko da aka yi bayan zamansa shugaban APC na kasa, Adamu ya ce "Nasarar alama ce ga nasarorin da ake tsammanin APC za ta samu a zaben jihar Osun a wannan shekarar kafin zuwan zabukan 2023."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban jam'iyyar ya mika jinjina ga shugaban kasa Muhammadu Buhari "wanda a matsayinsa na jagoran APC, ya samar da shawara tagari ga jam'iyyar a zaben jihar Ekiti".

Ya yi wa shugaban kasan alkawarin cewa, jam'iyyar za ta cigaba da bin dabarunsa wurin aiwatarwa a sauran zabukan gaba.

Kamar yadda shugaban ya ce, zababben gwamnan yana da gogewa da kuma hangen nesa da zai kai Ekiti mataki na gaba a fannin cigaba, Vanguard ta ruwaito.

Adamu ya kara da mika godiyarsa ga jama'ar jihar Ekiti ta yadda suka mika ragamarsu ga APC da Oyebanji, inda yayi alkawarin cewa zababben gwamnan zai cigaba da dabbakar da shirye-shiryen da suka shafi jama'a na jam'iyyar kamar yadda gwamna mai Baron gado, Dr. Kayode Fayemi ya fara.

Ya jinjinawa mambobin kamfen din APC na jihar Ekiti wanda Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi, kwamitin ayyuka na jam'iyyar a jihar da kuma magoya bayan jam'iyyar na jihar kan irin aikin kwazo, sadaukarwa da sa ido da suka yi wanda ya kai su ga nasara.

Shugaban jam'iyyar APC na kasa ya yi kira ga Oyebanji da tabbatar ya sauke nauyin da jama'ar Ekiti suka dora masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel