Muhimman Abubuwa 10 da Ya Dace a Sani Game da Zaben Gwamnan Ekiti

Muhimman Abubuwa 10 da Ya Dace a Sani Game da Zaben Gwamnan Ekiti

  • A ranar 18 ga watan Yuni, mutanen kwarai na jihar Ekiti zasu zaba sabon gwamnan da zai cigaba da jan ragamar jihar
  • Bai wuce saura kwanaki uku zaben gwamnan jihar ba, gasar zaben wanda zai gaji Kayode Fayemi sai kara kamari yake fiye da baya
  • Legit.ng ta tattara wasu abubuwa masu birgewa game da zaben jihar Ekiti wanda ya cancanci ku sani game manyan 'yan takara dake fafutukar ganin sun yi nasara

Zaben gwamnan jihar Ekiti na daya daga cikin manyan kanun labaran da ke jawo hirarraki a kan siyasa, a kashin farko bisa hudu na shekarar 2022.

Kafin babbar ranar Asabar, 18 ga watan Yuni, rashin iya hasashen wanda zai lashe zaben jihar ya yi kamari. Tun lokacin da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) sun ba wa gaba daya jam'iyyu 16 da zasu kara a filin zabe damar fara kamfen, wadanda suka dauki tsawon lokaci suna zagawa kananan hukumomin jihar don neman goyon baya da kuri'un jama'a.

Kara karanta wannan

Gwamnan Ekiti: Ba za mu karbi kudi ba, masu zabe sun dage, sun zargi APC da hauro da mutane don su yi zabe

Msu kada kuri'u sun fito kwan su da kwarkwata a jihar Ekiti
Muhimman Abubuwa 10 da Ya Dace a Sani Game da Zaben Gwamnan Ekiti. Hoto daga vanguardngr.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abubuwa da dama sun sa zaben zama abun burgewa, yayin da ya zama daga cikin manyan muhawara da tattaunawar siyasa, sai dai 'yan takarar duk sun karkata wajen ganin sun maye kujerar da tafi kowacce daraja a fadin jihar.

Duba da wannan lamarin, Legit.ng ta tattaro wasu abubuwan birgewa game da zaben jihar Ekiti da ake yi a ranar Asabar 18 ga watan Yuni.

1. Ranar zaben ta sha bamban da ta shekarar 2009

Kotun daukaka kara ta soke zaben gwamna Segun Oni bayan ya dauki sama da watanni 41 yana mulki. Kotun ta tabbatar da Kayode Fayemi a matsayin wanda ya lashe zaben tare da umartar su da su mika masa mulki cikin gaggawa. Sai dai INEC ta sake shirya kwaya-kwaryan zabe, wanda yasa Fayemi zama gwamnan jihar a shekarar 2010.

Kara karanta wannan

2023: Wike Ya Lashe Zaben Kwamitin Shawari Na Zaben Mataimakin Atiku a PDP

Da hakan ne tsarin zaben Ekiti ya canza.

2. Zabe kafin shekarar 2023

Zaben gwamnan Ekiti na daya daga cikin zaben gwamnoni a Najeriya da ke rigayar gaba daya zaben kasa.

Tsarin zaben Ekiti ya sauya ne yayin da kotun daukaka kara ta soke sakamakon zaben shekarar 2007 a shekarar 2019, daga nan ne ta sake fara kirga shekarun tabbata a madafun iko na tsawon shekaru hudu ga gwamnan jihar.

Masu zaben jihar na da wata dabi'ar zabe ba tare da dubi da jam'iyya ba sannan gwamnati ba ta cika maimaita kanta ba duk bayan shekaru hudu. Saboda haka, duk zaben gwamnonin Ekiti tun 1999 ya samar da gwamnoni daban-daban daga jam'iyyu daban-daban. Duba da wannan batun da sauran dalilai, wasu masu lura na ganin alamu na nuna zaben 18 ga watan Yuni na da wani salo da zai gabatar mai ban sha'awa.

Yayin da jam'iyya mai mulki ta APC karkashin mulkin Kayode Fayemi na fatan karya kwarin ta hanyar cigaba da mulki bayan zaben, inda jam'iyya mai adawa ke kokarin ganin ta jawo rudani.

Kara karanta wannan

Mataimakin shugaban kasa: Daga karshe Tinubu ya fayyace gaskiyar lamari kan tikitin Musulmi da Musulmi

3. Akwai 'yan takara 16 da zasu yi gogayya

Kamar yadda INEC ta bayyana, 'yan takarar da za su kara a zaben gwamnonin guda 16 ne. 'Yan takara mata guda biyu sune: Christiana Olatawura a jam'iyyar APP da Kemi Elebute-Halle ta ADP.

Ga jam'iyyar APC mai 'dan takara, wanda shine tsohon sakataran gwamnatin jihar da bai dade da sauka ba, Biodun Oyebanji, na kokarin ganin sun maye gurbin gwamnan tare da neman goyon baya daga gwamnati don ganin sun lashe zaben.

A PDP, tsohon gwamna Ayodele Fayose da kuma 'yar takarar jam'iyyar PDP, Bisi Kolawole, sun dauki tsawon lokaci suna kamfen din zaben.

A SDP, SDP ta yi fice a jihar yayin da tsohon gwamna Segun Oni ya yi takara a jam'iyyar. Ya yi gwamna tsakanin shekarar 2007 zuwa 2010.

A jam'iyyar ADC, 'dan takarar, Dr Wole Oluyede, wanda a da APC yake kafin ya fice daga jam'iyyar zuwa ADC don ya yi takarar gwamna.

Kara karanta wannan

Ekiti 2022: Jerin sunayen yan takara 16 da za su fafata a zaben gwamna

4. Manyan 'yan takara

Ba kamar sauran zabe a jihar Ekiti ba, na wannan shekarar ya sha bamban saboda ba jam'iyyu biyun da suka yi fice a Najeriya bane, PDP da APC, akwai sauran manyan 'yan takaran da ake magana a siyasa.

A takaice dai, zaben ba zai zama tsakanin dawakai biyun bane. Nasarar da Dr Wole Oluyede na ADC, tsohon gwamnan Segun Oni na SDP da Chief Reuben Famuyibo na Accord ya kara fadada gasar. Sai dai jam'iyyu biyu ne ke takara a zaben saboda yadda mutane za su yi zabe tare da dubi da fice da sauran dalibai wanda zai rage yawan 'yan takarar zuwa hudu.

Manyan 'yan takarar da ake tunanin za su kara su ne;

1. Biodun Oyebanji

2. Debo Ajayi

3. Bisi Kolawole

4. Tsohon gwamna Segun Oni.

5. Manyan jam'iyyun siyasa

A 'yan makonni da suka gabata, manyan jam'iyyun siyasar sun zafafaf kamfen domin samun amincewar masu kada kuri'y na jihar Ekiti.

Kara karanta wannan

Janar Abdulsalami Abubakar ya bayyana matsala 1 da za a iya samu a zaben 2023

Jam'iyyun sun hada da APC, PDP, da SDP. Sauran su ne AAC, ADC, ADP, APGA, APM, APP, LP, NNPP da NRM da sauransu.

6. Rumfunan zaben jihar Ekiti

Kamar yadda INEC ta bayyana, Ekiti tana da mutum 988,923 da suka yi rijistar katin zabe, amma 734,746 ne kadai suka karba a watan Mayun 2022.

Jihar tana da wurin rijista 177, rumfunan zabe 22,244 da kuma kananan hukumomi 16 a jihar.

7. Gwamnan dake kan karagar mulki

Gwamnan jihar Ekiti na yanzu, Kayode Fayemi, yana cika wa'adin mulkinsa karo ba iyu ne, don haka babu batun cewa gwamna na neman zarcewa.

8. Abubuwan a zasu iya sa APC ta zarce

Duk da APC ce ke mulkin jihar, babu tabbacin idan za ta cigaba da mulkin. Cigaban da ake samu a jihar ba shi da yawa saboda sauyin shugabanci.

Wasu daga cikin abubuwan da jam'iyyun adawa ke amfani da su wurin kamfen sun hada da:

Kara karanta wannan

Zaben Fidda Gwani: Yadda wasu 'Yan takaran APC suka kamu gaibu, suka sha kashi a hannun Bola Tinubu

-Walwalar 'yan fansho

-Tsaro

-Samar da ayyuka ga matasa

-Habaka tattalin arziki da sauransu.

9. Tsohon gwamna ya shiga tseren

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Segun Oni, wanda yayi mulki tsakanin 2007 zuwa 2010 ya shiga tseren a karkashin jam'iyyar SDP.

10. Zabukan da suka gabata a Ekiti

Abun birgewa ne idana aka sanar da mai karatu cewa, gwamnoni biyu, Ayodele Fayose da Kayode Fayemi ne kadai suka taba zarcewa da mulki a tarihin jihar Ekiti, amma sauran duk suna barin ofis ne bayan cikar wa'adin mulkinsu tun karo na farko.

Asali: Legit.ng

Online view pixel