Yobe North: Abin Da Yasa Muka Tura Wa INEC Sunan Ahmad Lawan, Shugaban APC, Adamu

Yobe North: Abin Da Yasa Muka Tura Wa INEC Sunan Ahmad Lawan, Shugaban APC, Adamu

  • Sanata Abdullahi Adamu ya bayyana cewa Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya yi takarar sanata a zaben fidda gwani na Yobe North
  • A cewar shugaban na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, na kasa, ba shi da lokacin martani kan batutuwa marasa dadi game da lamarin
  • Idan za a iya tunawa, Bashir Sheriff Machina ya yi ikirarin cewa shine ainihin dan takarar APC na mazabar Yobe North

A wani sabon cigaba da zai bawa yan Najeriya mamaki, Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana cewa shugaban majalisa Ahmad Lawan ya yi takara a zaben fidda gwani na Yobe North.

Adamu, wanda shine shugaban APC na kasa ya bayyana hakan ne yayin da ya jagoranci mambobin jam'iyyar don gabatar da zababen gwamnan Jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, ga Shugaba Muhammadu Buhari, The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ba zan yarda ba, Nuhu Ribadu ya shigar da kara kotu kan zaben fidda gwanin gwamnan Adamawa

Ahmad Lawan.
Yobe North: Abin Da Yasa Muka Tura Wa INEC Sunan Ahmad Lawan, Shugaban APC, Adamu. Hoto: Ahmad Lawan.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa, ba za iya martani kan duk wani jita-jita ba dangane da batutuwan da suka shafi jam'iyyar.

Lawan na daya daga cikin yan takarar shugaban kasa na APC guda 23 da suka yi takara a ranar 8 ga watan Yuni.

Bashir Machina ya yi ikirarin cewa shine dan takara na ainihi a jam'iyyar APC a mazabar Yobe North.

Da aka yi wa Adamu tambaya kan yadda Lawan ya zama dan takara, ya ce:

"Kada ka ja wa kanka zuwa kotu. Shin haka aka fada maka suke cewa? Ba ni da lokacin batutuwa marasa amfani. Ban da lokacin wannan. Idan ka tunkare ni da abubuwan alheri, ina da lokacinsu. Zan tsaya a nan in amsa dukkan tambayoyin ka.
"Ba zan iya martani kan kowane jita-jita ba, musamman mara alheri, wanda masu bita da kulle suka kirkira. Akwai wani doka da ya ce idan ka yi takara ba ka ci ba, ba za ka iya sake wani takarar ba?"

Kara karanta wannan

Rikicin takara: Ahmad Lawan ya gundiri mutane bayan shekaru 16 a Sanata Inji Hon. Machina

"Ka je ta nemi bayani daga wurin wanda ke shirya zaben fidda gwanin. Na yi nawa. Na sani, da kima ta, cewa ya yi zaben cikin lokacin da aka tanada."

Lawan vs Machina: Daga Karshe, INEC Ta Bayyana Matsayarta Kan Wanene Halastaccen Dan Takara

A bangare guda, hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta bayyana matsayanta kan rikici da ya barke kan tikitin takarar kujerar mazabar Yobe ta Arewa tsakanin Bashir Machina da Sanata Ahmad Lawan, Premium Times ta rahoto.

Daf da za a rufe karbar sunayen yan takara daga hannun jam'iyyun siyasa, rikici kan kujerar takarar Yobe ta Arewa a APC ya dauki hankula a yayin da Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawa da Bashir Machina wanda ake ganin ya ci zaben na APC ke ta kai ruwa rana.

Legit.ng ta tattaro cewa Lawan ya shiga takarar shugaban kasa tare da su mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, Rotimi Amaechi da Asiwaju Tinubu wanda shine ya lashe zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel