Tsohon Hadimin Jonathan Da Ya Yi Kaurin Suna Wurin Sukar Buhari Ya Nemi Afuwar Tinubu

Tsohon Hadimin Jonathan Da Ya Yi Kaurin Suna Wurin Sukar Buhari Ya Nemi Afuwar Tinubu

Reno Omokri, tsohon hadimin shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nemi afuwar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a zaben 2023, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Reno Omokri da Bola Tinubu.
Tsohon Hadimin Jonathan Da Ya Yi Kaurin Suna Wurin Sukar Buhari Ya Nemi Afuwar Tinubu. Hoto: @TheNation
Asali: Twitter

Omokri a watan Janairu ya zargi Tinubu da yawan fita kasashen waje don ganin likitoci idan ya kira shi 'Mai jinya a Landan".

"Tinubu ya ce ya tafi Landan don ya "huta". Ya ku yan Najeriya, shin ba ku gaji da yadda Buhari ke zuwa Landan don ya huta ba? Yanzu kuna son zaben Tinubu, wani mai jinyar Landan? Watanni uku da suka gabata Tinubu ya dawo daga Landan. Yanzu, ya koma! Ku yi tunani!".

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Dole Bola Tinubu Ya Fada Wa Yan Najeriya Yadda Ya Tara Dukiyarsa, In Ji Deji Adeyanju

Amma, Omokri, wanda ke da digiri a fanin karatun lauya ya canja ra'ayinsa, yana mai cewa ba dai-dai bane ya yi amfani da rashin lafiya don sukar Tinubu.

Ya kuma shawarci yan Najeriya su dena amfani da rashin lafiya wurin sukar yan siyasa.

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Juma'a, ya rubuta.

"Na taba amfani da rashin lafiyar Tinubu don sukarsa kuma na lura cewa idan ba mu mutu da kuruciya ba, dukkan mu za mu tsufa kuma wata kila mu yi fama da rashin lafiya.
"Don haka, ina neman afuwar Mr Tinubu da magoya bayansa. Duk da cewa rashin lafiyar dan takara na iya zama babban lamari, na yi alkawarin zan mayar da hankali kan wasu batutuwan banda rashin lafiyarsa daga yanzu. Allah ya muku albarka baki daya."
"Atiku, Tinubu da Obi suna shiri da juna fiye da shekaru 20.
"Don haka, ni da ku mu goyi bayan wanda muke so ba tare da gaba ba.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Saka Labulle Da Lawan Da Ameachi a Aso Rock Villa

"Zan yi wa dan takara na kamfen amma ba zan tilasta muku shi ba, Don Allah kuma ku yi hakan! Zabe zai zo ya tafi.
"Amma Najeriya tana nan, kuma idan Allah ya bamu tsawon rai, muma muna nan. Babu zagi, babu barazana, babu cin mutunci."

Ekiti 2022: 'Idan Ba Kuri'a, Ba Kudi', Bidiyon Tinubu Yana Yi Wa Masu Zabe Ba'a a Wurin Kamfen

A wani rahoton, Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a zaben 2023, Asiwaju Bola Tinubu, ya bukaci al'ummar Jihar Ekiti su fito su yi zabe idan ba hakan ba ba za a biya su ba.

Tinubu, wanda ya ziyarci a Jihar Ekiti a ranar Talata ya furta hakan ne wurin yakin neman zabe na dan takarar gwamna na jam'iyyar, Biodun Oyebanji gabanin zaben da ake shirin yi ranar Asabar 18 ga watan Yunin 2022.

Kara karanta wannan

Takarar Musulmi da musulmi: Ana yiwa Tinubu zagon kasa ne, in ji wani fasto

Ya kuma kambama kansa cewa bai taba fadi zabe ba a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel