Shugaba Buhari Ya Saka Labulle Da Lawan Da Ameachi a Aso Rock Villa

Shugaba Buhari Ya Saka Labulle Da Lawan Da Ameachi a Aso Rock Villa

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri tare da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi
  • Lawan da Amaechi dukkansu yan takara ne a zaben fidda gwani na shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC mai mulki da aka kammala a baya-bayan nan
  • Lawan ya bayyana cewa gwamnatin Buhari na iya kokarinta wajen warware matsalolin yan Najeriya sai dai mafi yawancin matsalolin sun gaje shi ne tun shekarar 1999

Shugaba Muhammadu Buhari, a daren ranar Lahadi a Aso Rock ya gana da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, kuma ya yi wata ganawar daban da shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan; dukkansu biyu tsaffin masu neman takarar shugaban kasa na APC a zaben fidda gwani da aka kammala.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya saki jerin sunayen jiga-jigan APC da wasu mutane da basa son Bola Tinubu

Taron na zuwa ne kwana biyu bayan dan takarar shugaban kasar na APC a zaben 2023, Bola Tinubu, ya gana da Buhari a Villa don masa godiya, rahoton The Punch.

Shugaba Buhari Ya Gana Da Lawan Da Ameachi a Aso Rock Villa
Buhari Ya Gana Da Lawan Da Ameachi a Abuja. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Matsalolin da muke fama da su an shuka su ne tun 1999 wasu ma kafin 1999, Lawan

Duk da cewa ba a bayyana abin da shugaban kasar ya tattauna da Amaechi ba, Lawan wanda ya yi magana bayan taron ya ce har yanzu jam'iyyar na fama da matsalolin da ta gada tun 1999.

"Ina son yi wa yan Najeriya alkawari a madadin jam'iyyata APC a matakin jiha da kasa cewa a koyaushe za mu yi abinda ya fi dacewa da rayuwar yan Najeriya kuma muna gazawa ne ba don muna so ba. Saboda muna fama da kallubale ne kuma shekarun mu takwas kacal.

Kara karanta wannan

Ba sauran hamayya: Yahaya Bello ya ba da tallafi mai tsoka ga ci gaban kamfen din Tinubu

"Akwai jam'iyyar da ta yi shekaru 16 a mulki kuma mafi yawancin matsalolin da APC ke fama da su a kasa da jiha matsaloli ne da aka shuka su lokaci mai tsawo tun 1999 wasu ma tun kafin 1999.
"Mun yi aiki sosai. Ina cikin manya a gwamnatin nan kuma na san nawa aka kashe wurin ayyukan raya kasa da karfafawa matasa," in ji shi.

Dukkansu tsaffin masu neman takarar shugaban kasar suna ziyararsu karo na farko ne bayan zaben fidda gwanin.

Kawo yanzu ba a fitar da sanarwa a hukumance ba bayan taron da suka yi.

El-Rufa'i: Buhari Ya Goyi Bayan Shawarar Da Muka Yanke Na Mayar Da Mulki Kudu a 2023

A wani rahoton, Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya dade yana goyon bayan matakin da gwamnonin arewa a APC suka dauka na mayar da mulki kudu a 2023.

Kara karanta wannan

Yadda Aisha Buhari ta Fice Daga Taron APC a Fusace, Ta ki Raka Buhari Mika wa Tinubu Tuta

Gwamnan na Jihar Kaduna ya bayyana hakan ne cikin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today a Channels Television.

Asali: Legit.ng

Online view pixel