Dole Bola Tinubu Ya Fada Wa Yan Najeriya Yadda Ya Tara Dukiyarsa, In Ji Deji Adeyanju

Dole Bola Tinubu Ya Fada Wa Yan Najeriya Yadda Ya Tara Dukiyarsa, In Ji Deji Adeyanju

  • Dan gwagwarmayar siyasa, Deji Adeyanju ya ce akwai bukatar Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ya fada wa yan Najeriya yadda ya tara dukiyarsa
  • Adeyanju ya ce akwai alamar tambaya a ga mutum kwatsam ya mallaki kudaden da har sun fi karfin motoccin daukan kudi kuma ba a san kasuwancinsa ko aikin da ya ke yi ba
  • Tun bayan da Tinubu ya zama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a zaben 2023, wasu masu sharhi kan siyasa sun rika saka alamar tambaya kan arzikinsa da lafiyarsa

Deji Adeyanju, dan gwagwarmayar siyasa kuma shugaban kungiyar 'Concerned Nigerians' ya ce akwai bukatar dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, ya fada ya yi bayanin yadda ya tara dukiyarsa, The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Musulmi da Musulmi: Yan Najeriya basu damu da addinin yan takara ba – Baba Ahmed

Adeyanju ya yi magana ne a baya-bayan nan cikin hira da aka yi da shi ta intanet a shirin 90MinutesAfrica - wanda Rudolf Okonkwo da Chido Onumah suka gabatar.

Asiwaju Ahmed Bola Tinubu.
Deji Adeyanju: Dole Bola Tinubu Ya Fada Wa Yan Najeriya Yadda Ya Tara Dukiyarsa. Hoto: @thecableng.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A ranar 8 ga watan Yuni an sanar da Tinubu matsayin dan takarar APC a zaben 2023 bayan ya lashe zaben fidda gwani da kuri'u 1,271.

Wasu masu sharhi kan harkokin siyasa sun yi ta maganganu kan takarar Tinubu, musamman batun kudinsa da kuma lafiyarsa.

Da ya ke magana yayin hirar, Adeyanju ya ce:

"Tinubu, tamkar Buhari, mai zuwa kasashen waje ne don duba lafiyarsa."

Ya kuma saka alamar tambaya kan arzikin Tinubu, yana cewa ya zama dole dan takarar shugaban kasar na APC ya fito fili ya yi bayani game da dukiyarsa da kasuwancinsa.

Kara karanta wannan

Takarar Musulmi da musulmi: Ana yiwa Tinubu zagon kasa ne, in ji wani fasto

"Kafin wani ya ce Tinubu ya shirya, kudi na gugan kudi kuma dala da dala, akwai bukatar su tambaya wani kamfani ya kafa ko kuma daga ina ya samo dukiyarsa," in ji shi.
"Wane ayyuka ko haja ya ke samarwa? Ta yaya kawai kwatsam mutum zai samu kudi masu yawa ta yadda har motoccin daukan kudi ba su iya dauka?"

Ekiti 2022: 'Idan Ba Kuri'a, Ba Kudi', Bidiyon Tinubu Yana Yi Wa Masu Zabe Ba'a a Wurin Kamfen

A wani rahoton, Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a zaben 2023, Asiwaju Bola Tinubu, ya bukaci al'ummar Jihar Ekiti su fito su yi zabe idan ba hakan ba ba za a biya su ba.

Tinubu, wanda ya ziyarci a Jihar Ekiti a ranar Talata ya furta hakan ne wurin yakin neman zabe na dan takarar gwamna na jam'iyyar, Biodun Oyebanji gabanin zaben da ake shirin yi ranar Asabar 18 ga watan Yunin 2022.

Kara karanta wannan

2023: Hadimin Ganduje Ya Bayyana Dalilan da Suka sa Ya Dace Ya Zama Mataimakin Tinubu

Ya kuma kambama kansa cewa bai taba fadi zabe ba a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel