Barazana da kalubale 9 da Bola Tinubu ya fuskanta wajen zama ‘Dan takaran APC a 2023

Barazana da kalubale 9 da Bola Tinubu ya fuskanta wajen zama ‘Dan takaran APC a 2023

  • Sai da aka yi ta gumurzu kafin a tsaida Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin ‘dan takaran APC
  • Wasu magoya bayan Bola Ahmed Tinubu sun ji tsoron Mai gidan na su ba zai samu tikitin 2023 ba
  • A karshe fitaccen ‘dan siyasar ya tashi da kuri’a sama da 1000 a zaben fitar da gwanin da aka yi

A wannan rahoto, mun bi diddikin yadda Bola Ahmed Tinubu ya yi ta fama da kalubale a kokarinsa na zama ‘dan takaran jam’iyyar APC a zaben 2023.

1. A sake kai takara Arewa

Akwai wasu a APC da suka nemi su bada shawarar a kai takara zuwa yankin Arewacin Najeriya ganin Atiku Abubakar ne ya samu tikitin jam’iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Zaben APC: Yadda Gwamnoni, Jagororin Arewa da ‘Yan NWC suka ba Bola Tinubu nasara

Da an yi hakan, Bola Tinubu ko wani ‘dan siyasan kudu ba zai yi nasara a zaben fitar da gwani ba.

2. Korafi gaban kwamiti

Tun da za a fara tantance masu neman takarar kujerar shugaban kasa a APC, sai wasu suka kai korafi gaban kwamitin da APC ta ba alhakin wannan aiki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An bukaci kwamitin ya yi waje da Bola Tinubu saboda zargin ya yi karya wajen yin takara a 1999.

3. An zaftare ‘yan takara 10

Daga baya an ji labari kwamitin John Oyegun ya cire sunan wasu daga cikin wadanda suka nemi takara, ya nuna APC ba za ta ba wanda ya tsufa takara ba.

Da farko, wannan labari ya tada hankalin magoya bayan Tinubu mai shekara 70 a Duniya.

4. Babu zaben fitar da gwani

Kafin a shiga zaben, an yi ta jita-jitar cewa Mai girma Muhammadu Buhari ya bukaci ‘yan takara su sasanta tsakaninsu, ta yadda ba sai an yi zaben tsaida gwani ba.

Kara karanta wannan

Manyan dalilai 4 da suka sa Tinubu ya lashe tikitin shugaban kasa na APC

5. Haduwar Gwamnoni da Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi zama da gwamonin jihohin APC, ya na neman su mara masa baya wajen fito da wanda zai karbi mulki daga hannunsa a 2023.

An ji tsoron shugaban kasar yana da wani ‘dan takara dabam ne da yake neman marawa baya.

‘Dan takaran APC
‘Dan takaran APC, Bola Tinubu Hoto: punchng.com
Asali: UGC

6. Ahmad Lawan ne ‘Dan takara

Ana daf da zaben fitar da gwani sai aka ji shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu ya ayyana Ahma Lawan a matsayin ‘dan takaran jam’iyya na shugaban kasa.

Kokarin kakaba Sanata Ahmad Lawan da sunan maslaha zai zama karshen burin Tinubu a APC.

7. Rage yawan ‘yan takara

A ranar da za ayi zaben tsaida gwani ne aka ji jam’iyyar APC mai mulki ta na kokarin rage yawan wadanda za su nemi takara daga mutane 23, zuwa biyar har zuwa uku.

A karshe dai ba a rage adadin wadanda suke neman tikitin ba, Tinubu ya dace da aka gwabza.

Kara karanta wannan

Tinubu da Atiku: Wurare 10 da aka samu kamanceceniya tsakanin manyan ‘yan takaran 2023

8. Mutane 3 sun janyewa Osinbajo

Sanata Kabiru Gaya ya fito yana fadawa Duniya cewa wasu ‘yan takara sun janyewa Yemi Osinbajo domin ya samu nasara a kan Bola Tinubu da sauran ‘yan takara.

Daga baya an fahimci hakan ba gaskiya ba ne, sai ma dai aka ji ana janyewa Tinubu takarar.

9. Tikitin Musulmi da Musulmi

Har zuwa filin zaben ‘dan takara ba a kyale Asiwaju Bola Tinubu ba, domin an rika yada furofaganda cewa ba zai dauki kirista idan aka ba shi damar takara ba.

Tinubu ya yi maza ya karyata wannan zargi, a karshe ya yi nasara da kuri’u 1, 200 a zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel