Da Dumi-Dumi: Yan takara uku sun janye wa mataimakin shugaban ƙasa

Da Dumi-Dumi: Yan takara uku sun janye wa mataimakin shugaban ƙasa

  • Daraktan kamfen na mataimakin shugaban kasa, Sanata Kabiru Gaya, ya ce wasu yan takara uku sun janye wa Osinbajo
  • Sanatan ya ce a halin yanzun sauran yan takara biyu kacal suka rage, Bola Ahmed Tinubu da Farfesa Yemi Osinbajo
  • A halin yanzun komai ya kankama a wurin taro bayan hallaran manyan mutane ana dakon fara kaɗa kuri'a

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Daraktan Kamfen na mataimakin shugaban kasa, Sanata Kabiru Gaya, ya ce yan takarar shugaban ƙasa a APC sun ragu zuwa mutum biyu, Farfesa Yemi Osinbajo da Bola Tinubu.

Punch ta rahoto Gaya na cewa yan takara guda uku daga ciki masu neman gaje Buhari sun janye wa mataimakin shugaban ƙasa.

Mataimakin shugaban ƙasa tare da Buhari.
Da Dumi-Dumi: Yan takara uku sun janye wa mataimakin shugaban ƙasa Hoto: Buhari Sallau/facebook
Asali: Facebook

Sanata Gaya mai wakiltar mazaɓar Kano ta kudu a majalisar datttawa, ya shaida wa Channels tv cewa masu neman kujerar shugaban ƙasa sun koma mutum biyu.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya magantu kan kowane ɗaya daga cikin yan takara 5 da gwamnoni suka kai masa

Sanata Gaya ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Yanzu muna da mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osimbajo, da Bola Ahmed Tinubu. Na samu labarin yan takara uku sun janye wa Osimbajo, Nnamani da wasu biyu sun janye wa Osinbajo."

Duk da jaridar ta gaza tabbatar da ikirarin sanatan, amma dai Nnamani ya sanar da janyewa daga takarar, inda ya bayyana hakan da siyasar yankin kudu maso gabas.

Kungiyar gwamnonin arewa sun miƙa wa shugaban ƙasa Buhari jerin yan takara 5 da suka ganin sun fi dacewa APC ta ba ɗaya tikitin takara.

Daga cakin yan takaran har da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Osinbajo da kuma jagoran APC na ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

An fara taro bayan zuwan Buhari

Bayanai sun bayyana cewa tuni kamai ya kankama ka'in da na'in tun bayan isar shugaba Buhari filin Eangle Square, Uwar gidansa, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari, ta isa filin.

Kara karanta wannan

Kebbi: Shugaban masu rinjaye a majalisa ya fice daga APC ya koma jam'iyyar PDP

Yanzu haka dai an fara baiwa kowane ɗan takara ɗaya bayan ɗaya dama su yi jawabi ga dukkan mahalarta taron da kuma Deleget masu kaɗa kuri'a.

A wani labarin kuma Zamu shiga tasku idan muka gaza zakulo ɗan takara mai ƙarfin Atiku, Gwamnan APC

Gwamnan Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce APC zata shiga matsala idan ba ta tsayar da wanda zai iya ja da Atiku ba.

Gwamnan ya ce ɗan takarar da PDP ta tsayar sananne ne kuma mai karfi dan haka wajibi APC ta yi karatun tanatsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel