Zaben fidda gwanin APC: Jerin mutum 13 da kwamitin tantancewa ta baiwa jam'iyya shawarar ta zaba

Zaben fidda gwanin APC: Jerin mutum 13 da kwamitin tantancewa ta baiwa jam'iyya shawarar ta zaba

Kwamitin mutum 7 da aka baiwa hakkin tantance yan takara kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sun zabi wasu mutum 13 cikin 23 da ya kamata a zaba.

Jiya kun ji cewa kwamitin ta gabatar da rahotonta shugaban uwar jam'yyar APC a Abuja.

Zaben fidda gwanin zai gudana ne ranar Litnin, 6 ga watan Yuni, 2022.

A ranar Juma'a, an ji rahotannin cewa kwamitin ta dakatad da yan takara 10 cikin 23.

Leadership tace majiyoyi daga fadar shugaban kasa sun bayyana cewa bau dan takarar da aka dakatar, kawai an bada shawara kan wasu 13 ne.

Kwamitin tantacewar ta baiwa APC shawara kan mutane 13 wadanda basu da wata matsala da ka iya kawowa jam'iyyar cikas idan dayansu ya lashe zaben.

Wadanda aka bada shawarar a zabi daya cikinsu sune:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

1. Asiwaju Bola Ahmed Tinubu;

2. Yemi Osinbajo;

3. Rotimi Amaechi;

4. Ahmad Lawan;

5. Yahaya Bello;

6. Kayode Fayemi;

7. Emeka Nwajiuba;

8. Dr Ogbonnaya Onu;

9. Ibikunle Amosun;

10. David Umahi;

11. Abubakar Badaru;

12. Godswill Akpabio;

13. Mr Tein Jack-Rich.

Zaben fidda gwanin APC
Zaben fidda gwanin APC: Jerin mutum 13 da kwamitin tantancewa ta baiwa jam'iyya shawarar ta zaba Hoto: Leadership
Asali: Facebook

Yan takara 10 da babu sunansu sune:

1. Pastor Tunde Bakare;

2. Rochas Okorocha;

3. Ben Ayade;

4. Sani Yerima;

5. Ken Nnamani.

6. Ikeobasi Mokelu;

7. Demeji Bankole;

8. Felix Nicholas,

9. Sen Ajayi Boroffice

10. Uju Ken-Ohanenye.

Asali: Legit.ng

Online view pixel