Manyan dalilai 4 da suka sa Tinubu ya lashe tikitin shugaban kasa na APC

Manyan dalilai 4 da suka sa Tinubu ya lashe tikitin shugaban kasa na APC

  • Zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki da ake ta zura idon zuwan shi ya zo har ya wuce
  • Bola Ahmed Tinubu ne ya lashe zaben bayan ya samu kuri’u 1,271 wajen lallasa babban abokin karawarsa Rotimi Amaechi wanda ya samu kuri’u 361
  • Sai dai kuma, akwai wasu manyan al'amura da suka taimaka wajen nasarar da Tinubu ya samu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Bayan an kai ruwa rana, Bola Ahmed Tinubu ne ya zama zakaran gwajin dafi a zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressive Congress (APC) mai mulki.

Duk da nasarar da Tinubu ya samu, ba abu ne mai sauki ba mallakar tikitin domin wakiltan jam’iyyar a takarar kujera ta daya mafi daraja a kasar.

Manyan dalilai 4 da suka sa Tinubu ya lashe tikitin shugaban kasa na APC
Manyan dalilai 4 da suka sa Tinubu ya lashe tikitin shugaban kasa na APC Hoto: APC
Asali: Facebook

Sai dai, akwai wasu abubuwa da suka taimaka wajen tabbatar Tinubu a matsayin zakaran gwajin dafi. Ga wasu manyan dalilai hudu da suka sa Tinubu ya samu kuri’u 1,271 wajen kayar da abokan hamayyarsa su 13 ciki harda mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo.

Kara karanta wannan

Tinubu da Atiku: Wurare 10 da aka samu kamanceceniya tsakanin manyan ‘yan takaran 2023

1. Zazzafan jawabi da Tinubu ya yi a Abeokuta

Ko shakka babu wannan na daya daga cikin lokutan da ba za a taba mantawa da su ba a tarihin Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tinubu ya ziyarci deliget din APC a Abeokuta, jihar Ogun yayin da yake kamfen dinsa na neman goyon bayan wakilan jam’iyyar.

A jawabinsa, ya bayyanawa deliget a fili cewa rawar ganin da ya taka shine ya kai shugaban kasa Muhammadu Buhari Aso Rock da ma gwamnan jihar Ogun mai ci, Dapo Abiodun.

A cewar jaridar TheCable, Tinubu ya yi ikirarin ziyartan Buhari a gidansa na Kaduna don bashi tabbacin cewa zai yi takarar shugaban kasa kuma zai yi nasara bayan ya gwada sau uku ba tare da nasara ba.

Ya ce:

“Ba don ni da na yi jagora ba, da Buhari bai yi nasara ba. Ya yi takara da farko, ya yi na biyu da uku amma duk ya fadi. Harma ya bayyana a talbijin cewa ba zai sake takara ba.

Kara karanta wannan

An yi kutse a shafin NNPC na Twitter, an yi amfani da shi wajen hasashen abokin takarar Tinubu

“Amma na je gidansa a Kaduna. Na fada masa za ka yi takara kuma za ka yi nasara, amma kada ka yi sakaci da lamarin Yarbawa.”

Wannan ikirari da ya yi a Abeokuta ya kasance cike da kwarin gwiwar ya nuna jajircewarsa da ra’ayinsa na son zama dan takarar jam’iyyar APC.

2. Rawar da Aisha Buhari ta taka

Mutane da dama basu san cewa uwargidar shugaban kasar ce ginshikin nasarar da Tinubu ya samu a zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC ba.

A cewar jaridar TheCable, jim kadan bayan furucin da Tinubu ya yi a Abeokuta, an tattaro cewa shugaban kasar ya yi fushi.

Majiyoyin sun ce yayin da take kare Tinubu, Aisha Buhari ta fada ma shugaban kasar cewa babu laifi a abun da ya fadi.

Majiyoyin sun kuma bayyana cewa da aka shiga awan zaben, uwargidar shugaban kasar ta hana mutane ganin maigidanta domin hana duk wani yunkuri na sauya masa ra’ayinsa.

Kara karanta wannan

Tinubu: Dole Mu Tabbatar PDP Ba Ta Sake Jin Kamshin Mulki Ba

3. Janyewar yan takara bakwai

Wannan wani lokaci ne mai muhimmanci a fafutukar neman tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC.

A filin Eagle Square a Abuja yayin da ake gudanar da babban taron APC, yan takara bakwai sun janyewa Tinubu, inda suka karkatar da kuri’un deliget dinsu zuwa wajen tsohon gwamnan na jihar Lagas.

Yan takara bakwai da suka janye masa sun hada da tsohon ministan harkokin Neja Delta Sanata Godswill Akpabio; tsohon gwamnan Ogun Sanata Ibikunle Amosun; Gwamnan Ekiti Kayode Fayemi; Gwamnan Jigawa Abubakar Badaru; tsohon kakakin majalisar wakilai Dimeji Bankole; mataimakin bulaliyar majalisar dattawa Ajayi Boroffice da mace daya tilo da ta tsaya takara, Uju Ohanenye.

4. El-Rufai da gwamnonin arewa 11

Kafin janyewar yan takara a filin taron, wasu abokan Tinubu sun yi wani shiri na gaggawa.

Wata ganawa da gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nadir El-Rufai ya jagoranta ya samu halartan gwamnonin arewa na APC su goma sha daya wadanda suka yarda a mika shugabancin kasar zuwa yankin kudu.

Kara karanta wannan

Kiristoci yan arewa 4 da dayansu zai iya zama abokin takarar Tinubu

Kamar yadda jaridar Premium Times ta rahoto, an tattaro cewa wannan ganawar ce ta sa Abubakar Badaru, gwamnan jihar Jigawa, ya janye daga tseren.

Gwamnonin sun hada da, Gwamna Aminu Masari (Katsina); Abubakar Sani Bello (Neja); Abdullahi Sule (Nasarawa); Babagana Zulum (Borno); Nasir El-Rufai (Kaduna); Muhammad Inuwa Yahaya (Gombe); Bello Matawalle (Zamfara); Simon Lalong (Filato); Abdullahi Ganduje (Kano); Abubakar Atiku Bagudu (Kebbi) da tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aliyu Wamakko.

Karshen tika-tiki: Kakakin kungiyar kamfen din Tinubu ya bayyana daga yankin da abokin takararsa zai fito

A gefe guda, kakakin kungiyar kamfen din Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnonin jam’iyyar APC na da yancin zabawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar abokin takara.

Da yake zantawa da jaridar The Punch, Bayo Onanuga, kakakin kungiyar kamfen din ya bayyana cewa abokin takarar Tinubu zai fito ne daga kowani bangare na yankin arewa kuma zai iya kasancewa daga kowani addini.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Malik Ado-Ibrahim ya lashe tikitin takarar a YPP ta su Adamu Garba

Onuga ya ce zai iya fitowa daga arewa maso gabas, arewa ta tsakiya ko kuma arewa maso yamma, kamar yadda jarida The Cable ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel