Babbar magana: An bukaci kwamiti ya kori Tinubu daga takaran shugaban kasa a APC

Babbar magana: An bukaci kwamiti ya kori Tinubu daga takaran shugaban kasa a APC

  • Yayin da ake ci gaba da tantance ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, wani dan jam’iyyar mai mulki na son a hana Asiwaju Bola Tinubu takara
  • Dan jam’iyyar APCn mai suna Sagir Mai Iyali ya ce kwamitin tantancewar ya haramtawa tsohon gwamnan Legas takara bisa wasu takardun karya da ya mika wa INEC a shekarar 1998
  • Iyali ya kuma yi ikirarin cewa ba a san shekarun Tinubu ba, inda ya kara da cewa rufa-rufa da ke tattare da shi zai iya kawo cikas ga damar APC a 2023

An bukaci kwamitin tantance 'yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC da ya kori Bola Tinubu, tsohon gwamnan Legas, saboda alamomin tambaya game cancantar iliminsa, TheCable ta ruwaito.

A wata wasika mai dauke da kwanan watan Mayu 17, 2022, wani Sagir Mai Iyali, wanda ya bayyana kansa a matsayin dan APC daga jihar Kano, ya roki jam’iyyar da ta haramtawa Tinubu takara kan wasu takardun karya da ya mika wa INEC a 1998.

Kara karanta wannan

Shirin zaben fidda gwani: Tinubu, wasu 11 sun tsallake tantancewar shugabannin APC

John Oyegun, tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa ne ke jagorantar kwamitin tantancewar, kuma ana ci gaba da atisayen ne a Transcorp Hilton da ke Abuja.

Ta kusa karewa Tinubu, an nemi korarsa a takar
Babbar magana: An bukaci kwamiti ya kori Tinubu daga takaran shugaban kasa a APC | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Iyali ya ce duk da cewa Tinubu ya haura shekarun da ake bukata na tsayawa takarar kujerar shugaban kasa, amma ba a san shekarunsa ba, inda ya kara da cewa rufa-rufa da ke tattare da Tinubu na iya jefa jam’iyyar ga rashin nasara a zabe mai zuwa, New Telegraph ta kawo.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Takardar da ya mika na cewa:

“Mun fahimci cewa Bola Ahmed Tinubu wanda tun daga lokacin ya siya fom din takararsa kuma ya mika wa jam’iyyar yana da wasu batutuwan da a fili da suke nuna irin wannan yanayin na rashin cancantar takara.
“Daga bayanan da ke kunshe a cikin abubuwan da ya gabatar a gaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC), musamman a shekarar 1999, Tinubu ya yi wata da’awar karya, a kan rantsuwar halartarsa a Jami’ar Chicago daga 1972-1976.

Kara karanta wannan

APC: Dan majalisan Arewa da ake zargi da badakalar kudin Korona ya rasa tikitin tazarce

“A bayyane yake yanzu cewa wadannan ikirari karya ne. Ba wai kawai an shigar da wannan ne a cikin fom na INEC tare da bayyana rantsuwar kotu a ranar 20 ga Disamba 1999 ba, yana ma kunshe a cikin wata takardar rantsuwar batan bayanai da aka gabatar a gaban babbar kotun Legas, rajistar Ikeja, ranar 29 ga Disamba, 1998."

Baya ga bijiro da wannan batu, takardar ta yi tsokaci da cewa, lallai Tinubu bai halarci jami'ar ta Chicago ba, kuma hakan barazana ne ga APC da kuma ya kamata kwamitin ya cire Tinubu daga takara.

Ba zan yi amai na lashe ba: Martanin gwamna Wike da ya sha kaye bayan ganawa da Atiku

A wani labarin, Gwamnan jihar Ribas kuma tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Nyesom Wike, ya jaddada cewa zai cika alkawarinsa ta hanyar marawa dan takarar shugaban kasa a PDP Alhaji Atiku Abubakar baya.

Kara karanta wannan

Da duminsa: EFCC ta gurfanar da Rochas Okorocha kan zargin damfarar N2.9bn

Wike a ranar Asabar jim kadan kafin a fara kada kuri’a a zaben fidda gwanin PDP ya yi alkawarin tallafa wa duk wanda ya samu nasara daga cikin masu neman tsayawa takara a jam'iyyar.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku ya lashe zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa da kuri’u 371 inda ya doke abokin takararsa mai bi masa, Gwamna Wike wanda ya samu kuri’u 237.

Asali: Legit.ng

Online view pixel