Abin da Tinubu ya fadawa Shugaban Majalisa a gaban kowa saboda ya nemi takara da shi

Abin da Tinubu ya fadawa Shugaban Majalisa a gaban kowa saboda ya nemi takara da shi

  • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu bai manta da Dr. Ahmad Lawan da yake jawabin samun nasara a APC ba
  • Bola Tinubu ya nuna bai ji haushi sosai saboda shugaban majalisar ya zama abokin takararsa ba
  • Jigon na APC ya taimakawa Lawan a siyasa, wannan bai hana Sanatan yin takara da shi a zabe ba

FCT, Abuja - ‘Dan takaran kujerar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya tabo Ahmed Lawan a jawabinsa na samun nasara.

Daily Trust ta ce a jawabin da ya gabatar a yammacin Laraba bayan ya zama ‘dan takaran APC, Asiwaju Bola Tinubu ya yi magana kan Ahmad Lawan.

Tsohon gwamnan na jihar Legas ya nuna fushinsa saboda tarayya da shi da Sanata Ahmad Lawan ya yi wajen zama ‘dan takaran APC a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Yadda Shugaban kasa ya nemi ya jawo kwamacala a APC wajen fito da ‘Dan takaran 2023

Bola Tinubu yake cewa yanzu komai ya wuce tun da Lawan ya sha kashi a zaben da aka yi.

“Ga ‘dan majalisa, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, da na dan ji haushi kadan saboda ka yi takara da ni.”
“Amma yanzu komai ya zama tarihi. Sai ka mike bayan damejin da aka yi maka.” - Bola Tinubu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tinubu da Lawan
Bola Tinubu tare da Shugaban Majalisa Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Kamar yadda rahoton da jaridar ta fitar ya bayyana, Bola Tinubu bai kare jawabinsa ba sai da ya yabawa Ahmad Lawan kan irin kokarin da yake yi a mulki.

Duk da ya nuna masa adawa wajen neman tikiti, jigon na jam’iyyar APC ya ce a matsayinsa na ‘dan majalisa, Lawan ya yi abin a yaba wajen cigaban kasa.

Tinubu ya taimaki Lawan

Za a iya cewa Tinubu ya taka rawar gani wajen zaman Ahmad Lawan shugaban majalisar dattawan a 2019, amma sai ga shi yana neman goge raini da shi.

Kara karanta wannan

An yi abin kunya: Bidiyon yadda Yahaya Bello ya kauracewa shugaban APC na kasa

A zaben 2015, jagoran na APC yana cikin wadanda suka marawa Lawan baya a majalisa, amma Bukola Saraki ne ya samu galaba a kan shi a wancan lokacin.

Lawan ya shiga zaben neman takarar shugaban kasa duk da ya fito daga Arewa, alhali gwamnonin yankin sun nuna goyon bayan a ba kudu takara.

Atiku zai doke Tinubu - PDP

Dazu aka samu labari, jam’iyyar PDP ta fito tana cewa Atiku Abubakar ya fi karfin Bola Tinubu, ba sa’arsa ba ne a siyasa don ya ma doke APC a zaben da aka yi a 2019.

Debo Ologunagba ya fito yana cewa jam’iyyar hamayyar za ta doke Asiwaju Bola Tinubu. A cewar kakakin na PDP, Atiku ya fi 'dan takarar da APC ta tsaida farin jini.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng