Yadda Shugaban kasa ya nemi ya jawo kwamacala a APC wajen fito da ‘Dan takaran 2023

Yadda Shugaban kasa ya nemi ya jawo kwamacala a APC wajen fito da ‘Dan takaran 2023

  • An shiga rashin tabbas a jam’iyyar APC a dalilin zabin ‘dan takarar kujerar shugaban kasa a 2023
  • Shugaban kasa ya ki sa bakinsa da wuri a kan wanda ya kamata jam’iyya ta ba tikiti a zaben badi
  • Wannan ya sa aka yi ta kai-komowa a jam’iyya, aka rasa wanda shugaban kasar yake tare da shi

Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki ta samu kanta a cikin mawuyacin hali wajen gudanar da zaben ‘dan takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2023.

Rahoton Daily Trust ya ce APC ta shiga kila-wa-kala da rashin tabbas a kan zabin ‘dan takara. Masu fashin baki su na ganin laifin shugaban kasa ne.

An yi ta kokarin tallata wasu ‘yan takara ga shugaba Muhammadu Buhari, amma shugaban bai bari ya ayyana wani daga cikinsu a matsayin zabinsa ba.

Kara karanta wannan

An yi abin kunya: Bidiyon yadda Yahaya Bello ya kauracewa shugaban APC na kasa

Har aka je daf da zaben fitar da gwani a ranar Talata, babu wanda ya san wanda shugaban kasan yake so ya zama magajinsa a watan Mayun shekarar 2023.

Babu abin da ya dame ni - Buhari

Idan za a tuna, da aka yi hira da Mai girma Muhammadu Buhari kwanakin baya a gidan talabijin, ya nuna bai damu da wanda zai zama shugaban kasa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da aka matsa masa, sai Buhari ya ce ba zai bari Duniya ta san wanda yake goyon-baya ba, don haka zai bar maganar a matsayin sirri ne cikin zuciyarsa.

Shugaban kasa
Muhammadu Buhari da manyan APC Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Muhammadu Buhari da manyan APC

Kwanan nan kuma sai aka ji Muhammadu Buhari yana mai rokon gwamnonin jihohi da su ba shi dama ya zakulo wanda zai yi takarar shugaban kasa.

Bayan nan sai Gwamnonin Arewa suka tsaida magana cewa duk wanda zai karbi shugabancin kasar nan ya fito daga bangaren Kudancin Najeriya.

Kara karanta wannan

Zaben fidda gwanin APC: Taro ya yi dumi, Osinbajo ya fice daga Eagle Square

Ahmad Lawan: Ta leko, ta koma

A ranar Litinin sai shugaban jam’iyya na kasa, Abdullahi Adamu ya bada sanarwar Ahmad Lawan a matsayin ‘dan takaran shugaban kasan da APC ta ke so.

Jim kadan da wannan sanarwa ne jawabi ya fito daga fadar shugaban kasa, aka ji Garba Shehu yana cewa Mai gidansa bai ayyana wani ‘dan takara ba.

Jawabin da ya fito daga fadar shugaban kasa ya nuna rashin goyon bayan a kakabawa jam’iyya ‘dan takara, akasin sanarwar da Abdullahi Adamu ya bada.

Wasu daga cikin ‘yan majalisar gudanarwa na jam’iyyar APC sun shaidawa Duniya cewa kan NWC bai hadu a kan a ba Sanata Ahmad Lawan takara ba.

A ba Kudu takara - Gwamna

Mai girma Abdulrahman AbdulRazaq ya bada uzurin rashin ganin sa hannunsa a takardar da Gwamnoni suka fitar a kan a mikawa Kudu mulki a 2023.

Gwamnan na jihar Kwara ya nuna yana tare da su Nasir El-Rufai da sauran Gwamnonin Arewa, Yahaya Bello ne kadai ya zama bare a cikin takwarorinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel