PDP tayi magana a kan 2023, ta yi hasashen yadda za ta kare tsakanin Atiku da Tinubu

PDP tayi magana a kan 2023, ta yi hasashen yadda za ta kare tsakanin Atiku da Tinubu

  • Jam’iyyar PDP ta fito tana cewa Atiku Abubakar ya fi karfin Bola Tinubu, ba sa’arsa ba ne a siyasa
  • PDP tayi magana a kan zaben ‘dan takaran shugaban kasa da jam’iyyar APC mai mulki ta gudanar
  • Jawabin da Debo Ologunagba na dazu ya nuna PDP ta dage a kan cewa Atiku ne ya lashe zaben 2019

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Jam’iyyar hamayya ta PDP ta fitar da jawabi a ranar Laraba, 8 ga watan Yuni 2022 a game da haduwar da za tayi da Asiwaju Bola Tinubu a 2023.

Rahoton da muka samu daga gidan talabijin na Channels TV ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ta fitar da jawabi dazu ta bakin kakakinta, Debo Ologunagba.

Mista Debo Ologunagba ya fito yana cewa jam’iyyar hamayyar za ta doke Asiwaju Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Babu daga kafa: Duk da Atiku ya taya shi murna, Tinubu ya bayyana abin da zai yiwa PDP a zaben 2023

A cewar Debo Ologunagba, ba a banza tsohon gwamnan na Legas ya samu takarar kujerar shugaban kasa a APC ba, amma ya ce ba zai kai labari ba.

“Jam’iyyar mu ta na tausayawa Asiwaju na kama hanyar da ba za ta kai shi ko ina ba, domin shi ba sa’an ‘dan takaran PDP wanda ya fi shahara, cancanta da shiryawa ba.”
“Mai girma Atiku Abubakar mai kokarin hada-kan al’umma, kuma zabin al’umma, wanda ya dankara shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da kasa a zaben 2019.”

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Asiwaju zai fahimci Najeriya ba irin sauran daulolin da ya mallaka ba ne, 'yan Najeriya ba karnukan siyasarsa ba ne kamar wadanda ya saye tikiti a hannunsu.”

- Debo Ologunagba

Atiku Abubakar
'Dan takaran PDP, Atiku Abubakar Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Tribune ta rahoto Sakataren yada labaran na PDP yana yin kaca-kaca da APC a jawabinsa, yana zargin kudi sun yi tasiri wajen tsaida 'dan takaran na 2023.

Kara karanta wannan

Peter Obi da Atiku ba su yi barci da wuri ba ba, sun yi magana a kan zaben ‘dan takaran APC

Ologunagba yake cewa jam’iyyar APC mai mulki ta gaza cika alkawuran da ta yi wa ‘yan Najeriya bayan shekaru bakwai da rantsar da Muhammadu Buhari.

A ra’ayin jam’iyyar adawar, Atiku Abubakar ne ya lashe zaben 2019 wanda aka fafata tsakanin sa da Muhammadu Buhari wanda ya tsayawa jam’iyyar APC.

Sai dai hukumar zabe ta tabbatar da Buhari ne ya yi nasara, wannan sakamakon ne kotu suka tabbatar. APC ta ba PDP ratar kuri'u sama da miliyan uku.

Zaben APC: Atiku da PDP sun yi magana

Dazu kun ji labari cewa Alhaji Atiku Abubakar ya tofa albarkacin bakinsa a kan zaben ‘dan takaran APC, ya ce jam'iyyar ba za ta iya kai labari a 2023 ba.

Haka zalika Peter Obi ya yi kira ga matasa yayin da APC ta ke fito da wanda zai yi mata takara a zaben 2023, ya ce su yi izina da mulkin Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Kebbi: Shugaban masu rinjaye a majalisa ya fice daga APC ya koma jam'iyyar PDP

Asali: Legit.ng

Online view pixel