An yi abin kunya: Bidiyon yadda Yahaya Bello ya kauracewa shugaban APC na kasa

An yi abin kunya: Bidiyon yadda Yahaya Bello ya kauracewa shugaban APC na kasa

  • Wani yanayi mai ban mamaki ya faru a yayin da APC ke ci gaba da gudanar da zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa
  • Yahaya Bello, ya bayyana a filin taro, amma ya ki gaisawa da shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu
  • Wannan lamari dai ya faru ne yayin da ake ci gaba da kai ruwa rana kan wanda ya dace APC ta tsayar a zaben 2023

Abuja - Jaridar PM News ta nuna wani bidiyo na Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi inda ya nuna kamar rashin mutuntawa ga shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu a zaben fidda gwani na shugaban kasa a jam'iyyar da ke gudana a dandalin Eagle Square dake Abuja.

Bello, wanda ya zo karramawa da gaisawa da shugabannin APC da gangan ya ki ya gaisa da Adamu, wanda shi ne kan-kat a shugabannin APC.

Kara karanta wannan

Kebbi: Shugaban masu rinjaye a majalisa ya fice daga APC ya koma jam'iyyar PDP

An yi abin kunya: Bidiyon yadda Yahaya Bello ya durkusa ya gaida kowa, amma kauracewa shugaban APC na kasa
An yi abin kunya: Bidiyon yadda Yahaya Bello ya kauracewa shugaban APC na kasa | Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Dan takarar shugaban kasan na jam’iyyar APC ya yi musabaha da tsaffin shugabannin jam’iyyar APC, John Odigie-Oyegun, Cif Bisi Akande da Adams Oshiomhole sannan ya wuce Adamu inda suka gaisa da Aisha Buhari da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Legit.ng Hausa ta lura cewa, Adamu ya kalli Bello cikin mamaki, cike da fushi ta yadda sai da ya gyara zama ya yi masa kallon kurilla.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Today Post NG ta sake yada bidiyon a shafinta na Twitter kamar haka:

Tun bayan fara batun yin sulhu a zabi dan takara daga yankin Kudu tare da bayyana Ahmad Lawan a matsayin dan takara Yahaya Bello da 'yan APC ke samun sabani.

Zaben fidda gwanin APC: Ba zan janye wa kowane dan takara ba, inji Yahaya Bello

A tun farko, Gwamnan jihar Kogi, kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, ya sha alwashin ba zai sake ya janyewa wani dan takara a zaben fidda gwani na shugaban kasa ba, yana mai cewa yana da kyakkyawar dama ta lashe zaben, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Shugaban PDP Ya Bayyana Abin Da Yasa Za Su Ci Zaben Shugaban Kasa Da Jihohi Da Dama a Najeriya

Bello na daga cikin mutane 10 da kwamitin Cif John Odigie-Oyegun ya tantance, har ta kai ga gwamnonin Arewa 13 suka yi shawarin mika tikitin takara zuwa Kudu tare da kara datse 'yan takara zuwa biyar ba tare da tuntubar 'yan takara ba.

Da yake magana da manema labarai a dandalin Eagle Square a gefen zaben fidda gwanin, ya ce ba zai janye ba saboda: “Ina da kyakkyawar dama ta lashe zaben fidda gwanin. Na tabbata ina da sama da 50% cikin 100% na deliget.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel