Da dumi-dumi: Mataimakin gwamnan Oyo ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

Da dumi-dumi: Mataimakin gwamnan Oyo ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

  • Mataimakin gwamnan jihar Oyo, Rauf Olaniyan, ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC
  • Olaniyan da kansa ne ya sanar da batun ficewar tasa a wata zantawa da ya yi da manema labarai a ranar Lahadi, 5 ga watan Yuni
  • Ya kuma bayyana cewa ko kadan hakan ba zai shafi huldarsa da Gwamna Seyi Makinde ba, yana mai cewa ba zai yi murabus daga kujerarsa ba

Oyo - Mataimakin gwamnan jihar Oyo, Rauf Olaniyan, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa All Progressives Congress (APC).

Olaniyan ya sanar da sauya shekar tasa ne a wata hira da manema labarai a ranar Lahadi, 5 ga watan Yuni, jaridar The Nation ta rahoto.

Da dumi-dumi: Mataimakin gwamnan Oyo ya sauya sheka daga PDP zuwa APC
Da dumi-dumi: Mataimakin gwamnan Oyo ya sauya sheka daga PDP zuwa APC Hoto: withinnigeria.com
Asali: UGC

Ya ce ya yanke hukuncin ne saboda amsa kiran magoya bayansa wadanda suka gaji da jira bayan suna ta jiran tsammani a PDP na tsawon lokaci.

Kara karanta wannan

Rikici: Zai zama bala'i idan APC ta hana Tinubu tikitin takarar shugaban kasa, Shettima

Sai dai kuma, ya bayyana cewa wannan sauya shekar tasa bata shafi alakarsa da gwamnan jihar, Seyi Makinde ba, yana mai cewa suna nan suna tafiya tare da gwamnan ta fuskacin shugabanci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma jadadda cewar ba zai yi murabus daga matsayinsa na mataimakin gwamna ba, Nigerian Tribune ta rahoto.

2023: El-Rufai, Zulum da sauran gwamnonin arewa masu goyon bayan kudu maciya amana ne – Kungiyar arewa

A wani labarin, wata kungiya mai kare muradin arewa ‘Northern Interests Coalition’ ta soki gwamnonin arewa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) su 10 wadanda suka goyi bayan mika mulki yankin kudu a 2023, jaridar Punch ta rahoto.

Kungiyar gwamnonin APC daga arewa ta goyi bayan kudu ta samar da shugaban kasar Najeriya na gaba a taron na ranar Asabar.

Kara karanta wannan

2023: Ban janye wa kowa takara ba, Gwamnan APC da ke mafarkin gaje Buhari ya magantu

Mambobin kungiyar sun hada da Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, Sule Abdullahi na jihar Nasarawa, Babagana Zulum na jihar Borno, Masari na Katsina, Abdullahi Ganduje na Kano, Solomon Lalong na Plateau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel