2023: Ban janye wa Osinbajo takara ba, Gwamna Fayemi ya karyata jita-jita

2023: Ban janye wa Osinbajo takara ba, Gwamna Fayemi ya karyata jita-jita

  • Gwamna Fayemi na Ekiti ya musanta raɗe-raɗin da ke cewa ya janye wa mataimakin shugaban kasa takara a APC
  • A wata sanarwa da ya fitar ta hannun daraktan Kamfen dinsa, gwamnan ya ce yana da goyon bayan masu ruwa da tsaki a APC
  • Ya yi kira da magoya bayansa ko ina suke su kwantar da hankalinsu yayin da za'a fafata zaben fidda gwani nan da yan kwanaki

Ekiti - Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya musanta rahoto da ke cewa yan janye daga takarar shugaban ƙasa ya bar wa mataimakin shugaba, Farfesa Yemi Osinbajo.

Daily Trust ta rahoto cewa gwamna Fayemi na ɗaya daga cikin yan takara da ke jiran ranakun 6,7, da 8 ga watan Yuni, domin fitar da ɗan takara ɗaya tilo a zaben fidda gwanin APC.

Kara karanta wannan

Gaskiyar bayani kan wanda Atiku Abubakar ya zaɓa ya zama matamakinsa a zaɓen 2023

Gwamna Kayode Fayemi.
2023: Ban janye wa Osinbajo takara ba, Gwamna Fayemi ya karyata jita-jita Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Wasu rahotanni sun yi ikirarin cewa Fayemi da wasu gwamnoni hudu sun gana da Osinbajo, inda ya amince ya janye wa mataimakin shugaban ƙasan.

Amma Fayemi, shugaban kungiyar gwamnoni (NGF) ya musanta rahoto a wata sanarwa ta hannun Daraktan Kanfen ɗinsa, Femi Ige, ranar Jumu'a.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mista Ige ya ce gwamnan ba zai janye wa kowane ɗan takara ba, yayin da ya ƙara da cewa yana da goyon bayan ƙusoshin jam'iyyar APC.

The Cable ta rahoto Ya ce:

"Ba bu wani taro da muka yi da wani ɗan takara game da zancen janye wa, ba tantama muna daga cikin yan takara da suka fi tabbas ɗin tikiti kuma ɗaya daga cikin yan takarar da za'a sanya wa ido."
"Ɗan takarar mu ya samu yarda da girma a tsakanksanin shugabannin jam'iyya da kuma takwarorinsa gwamnoni, waɗan da ke taka rawar gaban hantsi wajen yanke hukunci."

Kara karanta wannan

Rikici ya ɓarke a Sakatariyar APC ta Abuja bayan ɗan takarar shugaban kasa ya watsa kyautar N50,000

Daga ƙarshe gwamna Fayemi ya bukaci dandazon masoyansa su kwantar da hankulan su, ka da su cire rai saboda ita, "Ƙarya na habaka ne ta hannun masu son ɗauke hankali."

A wani labarin kuma Tinubu ya saki sabon Bidiyo, ya faɗi inda zai nufa idan ya sha ƙasa a zaɓen fidda gwanin APC

Bola Ahmed Tinubu ya bayyana hasashensa kan yadda sakamakon zaben fidda gwanin APC na takarar shugaban kasa ka iya kasancewa.

Jagoran APC na ƙasa ya gaya wa magoyan bayansa su sanya ransu a inuwa yayin da ya kammala duk abinda ya dace da zasu kai shi ga nasara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel