Rikici: Zai zama bala'i idan APC ta hana Tinubu tikitin takarar shugaban kasa, Shettima

Rikici: Zai zama bala'i idan APC ta hana Tinubu tikitin takarar shugaban kasa, Shettima

  • Kashim Shettima, tsohon gwamnan jihar Borno ya magantu kan matsayar tsagin Tinubu ga batun tikitin takara
  • Ya bayyana cewa, ba zai yiwa APC abu mai dadi ba idan aka hana tsohon gwamnan jihar Legas Tinubu tikitin takara
  • Ya bayyana haka ne yayin da yake kwaskwarima ga maganganun da Tinubu ya yi na cewa ya taimaki Buhari a zaben 2015

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kashim Shettima, tsohon gwamnan Borno, ya ce zai zama “bala'i” ga jam’iyyar APC idan ba a zabi Bola Tinubu ba, tsohon gwamnan Legas a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.

Ya fadi haka ne a ranar Juma’a, yayin da fito a wani shiri a gidan talabijin na TVC, TheCable ta ruwaito.

Shettima: Zai zama bala'i ga APC Tinubu ya rasa tikiti
Rikici: Zai zama bala'i idan APC ta hana Tinubu tikitin takarar shugaban kasa, Shettima | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

A cewarsa:

"Muna cikin wani yanayi na dimokuradiyya amma ina fargabar hakan na iya zama bala'i ga jam'iyyar."

Kara karanta wannan

Shirin 2023: APC ta magantu kan batun takarar Jonathan a zaben fidda gwanin shugaban kasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika, ya kuma bayyana cewa, shi mutum ne mai mai da hankali kan lamarru, haka kuma yana tabbacin Tinubu zai fito cikin jerin 'yan takara.

Da yake bayyana wasua dalilai, Shettima ya ce:

“Ba batun jayayya bane amma batun lokaci ne. Ya biya farashinsa, kuma a jiya a Abeokuta, ya yi wasu kalamai da aka gurbata da gangan kuma aka ambace su a kaikaice.
“Ko sun yarda ko ba su yarda ba, ya taka rawar gani ba kawai wajen fitowar shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin dan takarar jam’iyyar APC ba, a’a a zaben 2015 da ya gabata.”

Tsohon gwamnan na Borno ya kara da cewa idan Buhari zai zabi dan takara to Tinubu ne ya fi cancanta.

A cewar Shettima game da Buhari:

“Shi ne shugaban kasar nan. Gudunmawarsa na da matukar mahimmanci. Muna mutunta shi kuma muna girmama shi, amma mun yi imani a karshe, shugaban kasa mai bin tafarkin dimokuradiyya ne kuma zai daidaita kansa da muradun ‘yan jam’iyyarsa."

Kara karanta wannan

Hotuna: Daga karshe, an yiwa Ibrahim Magu karin girma zuwa AIG

Hakazalika, rahoton Daily Post ya bayyana cewa, shugaban kasa Buhari aboki ne na kut-da-kut da Tinubu, kuma zai zabe shi a amtsayin magaji.

Ga bidiyon da ke nuna lokacin da yake magana:

2023: Kwamitin tantancewar APC ya kori 10 daga cikin 'yan takarar shugaban kasa

A wani labarin, wani rahoton da This Day ta fitar ya ce, kwamitin tantance 'yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya kori mutane 10 da za su fafata a zaben fidda gwani da za a yi a mako mai zuwa.

Shugaban kwamitin, John Oyegun ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

A cewar Mista Oyegun, 13 ne kawai cikin 23 da kwamitin ya tantance za su fafata a zaben na mako mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel