2023: El-Rufai, Zulum da sauran gwamnonin arewa masu goyon bayan kudu maciya amana ne – Kungiyar arewa

2023: El-Rufai, Zulum da sauran gwamnonin arewa masu goyon bayan kudu maciya amana ne – Kungiyar arewa

  • Gamayyar kungiyar hadin gwiwa ta arewa ta yi watsi da gwamnonin APC 10 daga arewa kan goyon bayan mika shugabancin kasar ga yankin kudu a 2023
  • Kungiyar ta bayyana cewa sun aikata hakan ne saboda son zuciyarsu na son ganin sun zama mataimakin shugaban kasa
  • Sun kuma ja hankalinsu da su gaggauta janyewa daga wannan cin amanar da suke shirin yiwa yankin arewacin kasar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wata kungiya mai kare muradin arewa ‘Northern Interests Coalition’ ta soki gwamnonin arewa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) su 10 wadanda suka goyi bayan mika mulki yankin kudu a 2023, jaridar Punch ta rahoto.

Kungiyar gwamnonin APC daga arewa ta goyi bayan kudu ta samar da shugaban kasar Najeriya na gaba a taron na ranar Asabar.

Mambobin kungiyar sun hada da Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, Sule Abdullahi na jihar Nasarawa, Babagana Zulum na jihar Borno, Masari na Katsina, Abdullahi Ganduje na Kano, Solomon Lalong na Plateau.

Kara karanta wannan

2023: Kan Gwamnoni 10 a Arewa ya hadu, an samu Mutum na farko da ya janye takara a APC

Sauran sune Gwamna Abubakar Bello na Niger, Muhammad Inuwa na Gombe, Bello Matawalle na Zamfara, Abubakar Bagudu na Kebbi da tsohon gwamnan Sokoto, Aliyu Wamako.

2023: El-Rufai, Zulum da sauran gwamnonin arewa masu goyon bayan kudu maciya amana ne – Kungiyar arewa
2023: El-Rufai, Zulum da sauran gwamnonin arewa masu goyon bayan kudu maciya amana ne – Kungiyar arewa Hoto: Pulse Nigeria
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugaban kungiyar na Northern Interests Coalition, Malam Umar Gazali, ya bayyana cewa mutanen arewa sun yi watsi da hukuncin gwamnonin na cin amanar arewa.

A wata sanarwa da ya saki a ranar Asabar, Gazali ya zargi gwamnonin da hadewa arewa kai saboda son zuciyarsu.

Ya ce:

“Mun samu labarin ayyukan wasu gwamnonin arewa wadanda saboda son zuciyarsu na son zama mataimakin shugaban kasa, sun yanke shawarar matsawa shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya goyi bayan dan takarar shugaban kasa daga kudu a APC. Wannan cin zarafi ne kai tsaye ga arewa kuma ya zama dole a gaggauta dakatar da wadannan gwamnoni.
“Bayan mulki ya kasance kudu da ta samar da shugaban kasa tsawon shekaru 14 da mataimakin shugaban kasa tsawon shekaru 11 wanda gaba daya shekaru 25 kenan. Ba zalunci ne kawai ba, har ma da rashin hujja cewa gwamnoninmu za su yi wa Arewa makirci don ta rasa mulki bayan shekaru 8 kawai na shugabancin Buhari.”

Kara karanta wannan

Takarar Tinubu, Osinbajo, Amaechi da Lawan a 2023 ta na raba kawunan na-kusa da Buhari

A cewarsa, gwamnonin sun hada kai don matsawa shugaban kasa Buhari don ya goyi bayan ajandar son zuciyarsu.

Yayin da yake bayyana cewa arewa ta yi watsi da mugun nufinsu, ya sha alwashin cewa kungiyar hadin gwiwar da magoya bayanta a fadin yankin za su nuna musu turjuya.

Ya ce:

“Shawarar kawai da za mu ba gwamnonin da ke da hannu a wannan makircin shine su gaggauta janyewa. Ya zama dole shugaban kasar ya yi watsi da su sannan ya ki yarda wadannan maciya amanar arewar su batar da shi.

“Gwamnonin arewa 11 sun ci amanar arewa saboda son zuciyarsu. Mun yi Allah wadai da aikinsu kuma muna kara umurtan shugaban kasa da ya yi watsi da su kwata-kwata."

2023: Kan Gwamnoni 10 a Arewa ya hadu, an samu Mutum na farko da ya janye takara a APC

A wani labarin, gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar ya fita daga cikin masu neman kujerar takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Ni na ba ka mulki: Tinubu ya caccaki gwamna ido-da-ido kan goyon bayan Osinbajo

Kamar yadda Leadership ta fitar da rahoto, Muhammad Badaru Abubakar ne mutum na farko da aka ji ya janye takara a cikin masu neman shugaban kasa.

Gwamnan kuma mai neman yin takara a APC ya dauki wannan mataki ne bayan gwamnonin Arewa 10 sun hadu a kan a kai takara zuwa Kudu a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel