Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Bayyana Yankin Da Magajinsa Zai Fito a 2023

Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Bayyana Yankin Da Magajinsa Zai Fito a 2023

  • Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce yankin kudancin kasar ce za ta fitar da wanda ya ke son ya gaje shi a 2023
  • Buhari ya bayyana hakan ne yayin wani taro da ya yi da masu neman takarar shugabancin kasa a jam'iyyar APC a ranar Asabar gabanin zaben fidda gwani
  • Shugaban kasar ya ce hakan shine karamci kuma zai tabbatar da hadin kai da karfafa jam'iyyar ta APC a yayin da ta ke tunkarar babban zaben na 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Asabar ya ce yankin kudancin Najeriya ta fitar da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a babban zaben 2023, rahoton The Punch.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin taron da ya yi da masu neman takarar shugaban kasa a jam'iyyar mai mulki.

Kara karanta wannan

Manyan matsaloli 4 da ke gaban APC yayin da zaben fidda gwani ya gabato

Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Bayyana Yankin Da Magajinsa Zai Fito a 2023
Buhari ya ce kudu ce za ta fitar dan takarar da ya ke fatan zai gaje shi a 2023. Hoto: @thecableng.
Asali: Twitter

The Cable ta fahimci cewa shugaban kasar ya ce bangaren Action Congress of Nigeria, ACN, na jam'iyyar ya fitar da dan takarar shugaban kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin taron, Buhari ya bukaci gwamnonin jam'iyyar APC da masu neman takarar shugaban kasar su kasance cikin shiri domin zaben fidda gwani, hakan na nufin babu batun sassanci.

Wasu daga cikin yan takarar, The Cable ta fahimci, sun janye takararsu a wurin taron.

A yayin wani taro da shugaban kasar ya yi da gwamnonin a ranar Talata, Buhari ya bukaci a rama wa kudu karamci wurin zaben magajinsa.

"Bisa tsarin siyasar cikin gida na wannan jam'iyyar kuma a yayin da muke tunkarar zaben fidda gwani cikin yan kwanaki, ina neman goyon bayan gwamnoni da masu ruwa da tsaki wurin zaben magaji na, wanda zai rike tutar jam'iyyar mu a zaben shugaban kasar tarayyar Najeriya a 2023.

Kara karanta wannan

Babu dan takarar da aka cire, dukkansu zasu gana da Buhari da daren nan: Adamu

"Ina son tabbatar muku cewa za mu cigaba da tuntuba domin ganin cewa dukkan masu neman takara da masu ruwa da tsaki an tafi da su tare har zuwa taron gangami.
"Hakan zai kwantar da hankulan yan jam'iyya kuma jam'iyyar mu za ta yi nasara," in ji Buhari.

Baya ga mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu, sauran yan takarar sun hada da Sanata Lawan Ahmad da tsohon minista Rotimi Amaechi, Ogbonnaya Onu, Godswill Akpabio da Chukwuemeka Nwajiuba.

Saura sun hada da Sanata Ken Nnamani, Dimeji Bankole, Ibikunle Amosun, Ajayi Boroffice da Rochas Okorocha.

Abokin takarar Buhari a zaben 2011, Fasto Tunde Bakare, Uju Ken-Ohanenye, Nicholas Felix, Ahmad Rufai Sani, Tein Jack-Rich da Ikeobasi Mokelu suma suna cikin yan takarar shugaban kasar.

Ba Mu Gamsu Da Neman Afuwar Tinubu Ba, APC Za Ta Hukunta Shi Kan Maganganun Da Ya Faɗa Kan Buhari, Adamu

A wani rahoton, Shugabancin jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ta ce akwai yiwuwar za ta hukunta jagoranta na ƙasa kuma mai neman takarar shugabancin kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, saboda maganganun da ya furta kan Shugaba Muhammadu Buhari ƴan kwanaki da suka wuce, Leadership ta rahoto.

Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa Sanata Abdullahi Adamu, ne ya furta hakan yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi a sakatariyar Jam'iyyar APC a Abuja a ranar Asabar

Asali: Legit.ng

Online view pixel