Babu dan takarar da aka cire, dukkansu zasu gana da Buhari da daren nan: Adamu

Babu dan takarar da aka cire, dukkansu zasu gana da Buhari da daren nan: Adamu

  • Shugaban jam'iyyar APC ya karyata rahotannin cewa sun tsige mutum goma cikin wadanda tantance
  • Mutum ashirin da uku suka siya Fam din takara kujerar shugaban kasa karkashin jami'yyar APC
  • Kowanne cikin wadanda mutanen 23 ya biya kudi Naira milyan dari don sayen Fam

Abuja - Shugaban uwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) Sanata Abdullahi Adamu ya yi watsi da rahoton kwamitin tantance yan takarar kujerar shugaban kasa da ya cire yan takara 10 cikin 23 da suka yanki Fam.

Ya ce kwamitin gudanarwar jam'iyyar APC bata tsige ko mutum guda cikin yan takara 23 da aka tantance ba.

A cewar TheNation, yayin hira da manema labarai ranar Asabar, Adamu yace:

"Ina son bayyana cewa babu dan takaran da aka dakatar. Kamar jarabawa ne. Ko da mutum ya ci, akwai wadanda zasu zo na daya zuwa wadanda zasu yi na karshe."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: APC Za Ta Hukunta Tinubu Kan Maganganun Da Ya Yi Game Da Buhari, Adamu

"Saboda haka babu dan takaran da aka dakatar. Kuma gashi ma shugaban kasa ya gayyacesu duka cin abincin dare yau."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kwamitin tantancewa
Babu dan takarar da aka cire, dukkansu zasu gana da Buhari da daren nan: Adamu Hoto: Rotimi Amaechi
Asali: Twitter

Zaben fidda gwanin APC: Jerin mutum 13 da kwamitin tantancewa ta baiwa jam'iyya shawarar ta zaba

Kwamitin mutum 7 da aka baiwa hakkin tantance yan takara kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sun zabi wasu mutum 13 cikin 23 da ya kamata a zaba.

Wadanda aka bada shawarar a zabi daya cikinsu sune:

1. Asiwaju Bola Ahmed Tinubu;

2. Yemi Osinbajo;

3. Rotimi Amaechi;

4. Ahmad Lawan;

5. Yahaya Bello;

6. Kayode Fayemi;

7. Emeka Nwajiuba;

8. Dr Ogbonnaya Onu;

9. Ibikunle Amosun;

10. David Umahi;

11. Abubakar Badaru;

12. Godswill Akpabio;

13. Mr Tein Jack-Rich.

Yan takara 10 da babu sunansu sune:

Kara karanta wannan

Babu 'dan takarar da APC ta yi watsi da shi yayin tantancewa, Mamban Kwamitin Tantancewa

1. Pastor Tunde Bakare;

2. Rochas Okorocha;

3. Ben Ayade;

4. Sani Yerima;

5. Ken Nnamani.

6. Ikeobasi Mokelu;

7. Demeji Bankole;

8. Felix Nicholas,

9. Sen Ajayi Boroffice

10. Uju Ken-Ohanenye.

Asali: Legit.ng

Online view pixel