Ba Mu Gamsu Da Neman Afuwar Tinubu Ba, APC Za Ta Hukunta Shi Kan Maganganun Da Ya Faɗa Kan Buhari, Adamu

Ba Mu Gamsu Da Neman Afuwar Tinubu Ba, APC Za Ta Hukunta Shi Kan Maganganun Da Ya Faɗa Kan Buhari, Adamu

  • Sanata Abdullahi Adamu, shugaban jam'iyyar APC na kasa ya ce akwai yiwuwar jam'iyyar za ta hukunta jagoranta na kasa Asiwaju Bola Tinubu saboda maganganun da ya yi kan Buhari
  • Sanata Adamu ya bayyana hakan ne yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi a sakatariyar APC na kasa a ranar Asabar
  • Tinubun, ya furta maganganu da ke nuna cewa ba don shi ba Buhari da wasu gwamnoni ba za su ci zabe ba duk da cewa daga bisani ya fitar da karin bayani yana cewa ba don raini ya furta hakan ba

Shugabancin jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ta ce akwai yiwuwar za ta hukunta jagoranta na ƙasa kuma mai neman takarar shugabancin kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, saboda maganganun da ya furta kan Shugaba Muhammadu Buhari ƴan kwanaki da suka wuce, Leadership ta rahoto.

Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa Sanata Abdullahi Adamu, ne ya furta hakan yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi a sakatariyar Jam'iyyar APC a Abuja a ranar Asabar.

Ba Mu Gamsu Da Neman Afuwar Tinubu Ba, APC Za Ta Hukunta Shi Kan Maganganun Da Ya Faɗa Kan Buhari, Adamu
Adamu: Akwai yiwuwar APC za ta hukunta Tinubu saboda maganganun da ya yi game da Buhari. Hoto: @LeadershipNGA.
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Idan za a iya tunawa Tinubu yayin ziyarar da ya kai Jihar Ogun don ganawa da daligets a ranar Alhamis, an gan shi a bidiyo a ranar Talata yana cika baki cewa shi ya taimaka wa Shugaba Buhari da wasu suka ci zabe a baya.

Duk da cewa Tinubu ya fitar da sanarwar na yin karin bayani kan abubuwan da ya faɗa kan shugaban kasar a ranar Juma'a. Amma, Adamu ya ce wannan bada hakurin bai isa ba.

"Akwai yiwuwar za mu hukunta shi (Tinubu) saboda maganganun da ya faɗa kan Shugaban Kasa," in ji Adamu.

Osinbajo Ya Yi Ganawar Sirri Da Shugaban APC Da Gwamnoni 5 a Ofishinsa

A bangare guda, Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, a halin yanzu yana ganawa da a akalla gwamnonin jam'iyyar APC guda biyar da Sanata Abdullahi Adamu shugaban jam'iyyar APC na ƙasa a ofishinsa.

Taron na zuwa ne kwanaki biyu bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da gwamnonin a dakin taro na Council Chambers a gidan gwamnati a ranar Talata kafin ya tafi Madrid, Spain.

Hakan kuma na zuwa ne bayan kammala tantance yan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC da kwamitin John Odigie-Oyegun ta yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel