Manyan matsaloli 4 da ke gaban APC yayin da zaben fidda gwani ya gabato

Manyan matsaloli 4 da ke gaban APC yayin da zaben fidda gwani ya gabato

  • Jam'iyya mai mulki ta APC na tsaka mai wuya game da daukar 'dan takara a zaben fidda gwanin jam'iyyar da za a gabatar cikin kwanakin nan
  • Sai dai, bama wannan kadai ba, kudu ta hurawa shugaban kasa Muhammadu Buhari wuta a kan cewa lokaci ya yi da za ba ta damar fidda 'dan takarar shugaban kasa
  • Haka zalika, Ibon kudu sun lashi takobin kin marawa duk dan takarar da ya fito daga arewa, sannan sun bukaci jam'iyyar ta fiddo da 'dan takara daga kabilar su

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jam'iyya mai mulki ta shiga matsanancin rudani a kan zaben wanda zai rike tutar takarar shugaban kasa zaben shekarar 2023.

Rudanin ya kara kamari ne tun lokacin da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya zama zakaran gwajin dafin jam'iyyar adawa ta PDP, hakan yasa APC ke nazarin ganin ta zabi 'dan takarar da zai iya gogayya har ya lallasa don ganin jam'iyyar ta cigaba da mulki.

Kara karanta wannan

2023: Muhimman dalilai 3 da za su iya sa Tinubu ya rasa tikitin takarar shugaban kasa a APC

Kamar yadda jam'iyyar ke shirye-shiryen zaben fidda gwaninta da zata gabatar a ranar 6 zuwa 8 ga watan Yuni, Daily Trust a kula da manyan matsaloli hudu da ke tunkaro zaben.

Daga wanne bangare Buhari zai dauki magajinsa?

Idan 'dan takarar shugaban kasar arewa ya lashe zaben fidda gwanin, kungiyoyin kudu irinsu Afenifere, Pan Niger Delta Forum (PANDEF), Ohanaeze Ndigbo, Kungiyar Middle Belt da kungiyar kudanci da ta shugabannin Middle Belt ba zasu ji cewa suna da wata kima a APC ba.

Gwamnan jihar Ondo kuma shugaban kungiyar gwamnonin kudu, Rotimi Akeredolu, ya ce a ranar 4 ga watan Mayu dole APC ta yi amfani da tsarin karba-karban yankuna, inda ya tsaya a kan cewa yanzu lokaci yayi da za a bawa 'yan kudu damar fidda 'dan takarar shugaban kasar Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Shugabanci a 2023: Obasanjo na bakin ciki da yadda Atiku ya samu tikitin takara a PDP, yana shirya masa tuggu

"Yana da kyau mu guji jefa kawunanmu a rikice-rikice kafin gangamin zabe mai karatowa. Yanzu lokaci ya yi da kudancin kasar nan za ta samar da 'dan takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa. Dole a yi hakan ba tare da jinkiri ba. Na dokar tsarin tarayya da kundin tsarin mulki na 1999 wanda aka wa kwaskwarima. Ba adalci bane wani ya kalubanci wannan tsarin karba-karban wannan lokacin," a cewarsa.

Tashin hankalin kudu maso yamma

Biyu daga cikin 'yan takarar shugaban kasa a APC, Yemi Osinbajo da Ahmad Bola Tinubu, duk daga kudu maso yamma suke. Yayin da Tinubu ya kasance tsohon gwamnan jihar Legas kuma jagoranci jam'iyyar APC, Osinbajo shi ne mataimakin shugaban kasa, hakan yasa duka biyun suke cikin manyan masu fadi aji a jam'iyyar, kuma da yankin kudu maso yamma.

Idan jam'iyyar ta tsaya a kan yin zabe, damar samun kuri'un wakilan zaben kudu maso yamma ya rabu a kan wanda za su zaba tsakanin 'yan takarar biyu.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen 'yan takara 5 da ake sa ran Buhari zai zabi daya don ya gaje shi

Haka zalika, akwai wasu 'yan takara irinsu gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti, tsohon kakakin majalisar dattawa Dimeji Bankole, Fasto Tunde Bakare da tsohon gwamnan jihar Ogun kuma sanata mai ci, Ibikunle Amosun wadanda za su yi kokarin ganin sun samu kuri'un wakilan zabe daga yankin.

Tsarin karba-karba da damuwar kudu maso yamma

Baya ga hurawa APC wuta don ganin ta ba wa kudu tiketin, alamu na nuna cewa 'dan takarar shugaban kasar zai fito daga kudu ne.

Yankin sun ji tsoron PDP bayan Atiku ya zama zakaran gwajin dafin jam'iyyar, inda suka lashi takobin kin mara masa baya.

Shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta duniya a wata takarda da ta fitar ranar Alhamis ta bayyanawa shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa kudu maso yamma baza ta amince da duk 'dan takarar shugaban kasar da ya fito daga yammacin kasar, inda suka bukaci shugaban kasar ya nada dan takara daga kabilar Igbo.

Kara karanta wannan

2023: Atiku ya nemi hadin kan Wike, Saraki da sauran jiga-jigan PDP don lallasa APC

"Mun ga gadar Neja ta biyu wacce ake gab da gamawa kuma muna godiya ga shugaban kasa Muhammadu game da wannan, kuma mu Ibo zamu cigaba da biyayya ga shugaban kasa idan ya marawa 'dan kudu daga kabilar Ibo baya wanda zai gajeshi a shekarar 2023.
"Saboda haka ne Ohanaeze Ndigbo ta duniya take rokon APC da shugaban jam'iyyar mai mulki, shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya zabi zaman lafiya, hadin kai da kwanciyar hankali sama da sauran dalilai wajen ganin ya zabi Ibodaga kudu maso gabas ko Ikwerre a jihar Ribas, a matsayin rigakafin da zai kawo warakar ga hadin kan Najeriya," kamar yadda takardar da babban sakataran Ohanaeze Ndigbo ta duniya, Mazi Okechukwu Isiguzoro ta bayyana.

Abun tambaya game da zaman sulhu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci gwamnonin jam'iyyar APC da su zabi wanda ya dace ya gajeshi a ganawar da suka yi a Aso Rock ranar Talata.

Kara karanta wannan

2023: Buhari ya lissafa sharuddan da dole 'dan takarar shugabancin kasa na APC ya cika

Ya ce da gwamnonin, "Jam'iyyar ta yi nasarar samar da dokokin cikin gida don kawo cigaba ga shirye-shiryen gadar shugaban cikin kwanciyar hankali ko a matakin jihar da kananan hukumomi
"Yayin amfani da dokokin cikin jam'iyya, sannan bayan dubi da zaben fidda gwanin da zau gabata kwanaki kalilan masu zuwa, ina bukatar goyon bayan gwamnonin da sauran masu rike da mukamai wajen zaben magaji na, wanda zai rike tutar jam'iyyarmu a zaben mai karatowa a matsayin shugaban tarayyar Najeriya a 2023."

Asali: Legit.ng

Online view pixel