2023: APC Da PDP Sun 'Tashi Aiki', Labour Party Za Ta Lallasa Su, Doyin Okupe

2023: APC Da PDP Sun 'Tashi Aiki', Labour Party Za Ta Lallasa Su, Doyin Okupe

  • Dr Doyin Okupe, Shugaban Kungiyar Kamfen Din Shugaban Kasa na Peter Obi ya ce Labour Party ne za ta yi nasara a zaben 2023
  • Okupe ya ce jam'iyyun APC da PDP sun gama amfani da Najeriya domin ba su da abin da yan kasa da matasa ke nema don haka ba za su ci zabe ba
  • A cewar Okupe jam'iyyar PDP ta kauce daga turbar da mazan jiya da suka kafa ta na karba-karba hakan yasa ba za ta yi nasara ba a babban zaben mai zuwa a 2023

Ogun - Shugaban Kungiyar Kamfen Din Shugaban Kasa na Peter Obi, Doyin Okupe ya ce jam'iyyun APC da PDP sun gama tashensu kuma masu zabe ba za su sake kula su ba.

Okupe ya ce, jam'iyyar Labour Party, wacce Obi ke takarar a karkashinta ne za ta ci galaba kan manyan jam'iyyun biyu a Najeriya ta karbi ragamar mulkin kasar a 2023.

Kara karanta wannan

Sakon Obi ga matasan Najeriya: Ya rataya a wuyanku ku kori PDP da APC a 2023

2023: APC Da PDP Sun Tashi Aiki, Labour Party Za Ta Lallasa Su, Doyin Okupe
2023: APC Da PDP Sun Tashi Aiki, Labour Party Za Ta Lallasa Su, Doyin Okupe. Hoto: @VanguardNGR.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa ya bayyana hakan ne yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi jim kadan bayan kammala taro da shugabannin Labour Party a Abeokuta, Jihar Ogun.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Obi, wanda ya fice daga PDP a baya-bayan nan kan rashin bawa yankin kudu tikitin takara ya zargi jam'iyyar da 'rashin kyautatawa da rashin adalci'.

Wadanda suka yi watsi da karba-karba ne suka rushe jam'iyyar PDP, Okupe

Okupe ya jaddada cewa wasu daidaikun mutane da suka ki amincewa da tsarin karba-karba sun kaucewa turban da mazan jiya da suka kafa jam'iyyar suka dora ta a kai.

Okupe ya jadada cewa Obi zai lallasa APC da PDP, yana dogaro da mutanen Najeriya, matasa, yan kasuwa maza da mata da wasunsu.

Wani sashi na jawabinsa:

Kara karanta wannan

2023: 'Yan Kudu Surutu Kawai Suka Iya, Arewa Za Ta Fitar Da Shugaban Ƙasa, In Ji Babban Fasto a Najeriya

"Magabantanmu sun kafa jam'iyyar PDP kan turba mai kyau. Wasu da suka zo jiya suka ce karba-karba bata da muhimmanci sun rusa jam'iyyar PDP. Sun kaucewa tsarin nasara da sa'a don sun zama marasa adalci da son gaskiya.
"Babu wani tsari na rashin gaskiya da adalci da zai yi nasara. PDP jam'iyya ce mai kyau a baya amma yanzu ta lalace. APC kuma tunda farko ba ta da kyau, ba su da wani tasiri. Jam'iyyun biyu sun fita, sun lalace, ba su da abin da yan Najeriya da matasa ke nema."

Katsina Ba Ta Siyarwa Ba Ce, Ɗalibai Ga Wakilan Jam'iyyu

A wani rahoton, Kungiyar Hadin Kan Daliban Jihar Katsina ta shirya zanga-zangar lumana musamman ga wakilan manyan jam’iyyu akan su zabi ‘yan takarar gwamna na kwarai wadanda za su ciyar da jihar gaba.

Daily Trust ta ruwaito cewa daliban sun dinga zagaye manyan titinan da ke garin Katsina rike da takardu wadanda su ka rubuta, “Jihar Katsina ba ta siyarwa ba ce”.

Kara karanta wannan

Na Yi Matuƙar Takaicin Yadda Daliget Ɗin Jihar Mu Ba Su Zaɓe Ni Ba, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na PDP

Yayin zantawa da manema labarai, shugaban daliban, Aliyu Mamman, ya nemi wakilan su duba zabin da ke zuciyoyin mutanen jihar wadanda su ka zarce mutane miliyan takwas a zuciyarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel