Sakon Obi ga matasan Najeriya: Ya rataya a wuyanku ku kori PDP da APC a 2023

Sakon Obi ga matasan Najeriya: Ya rataya a wuyanku ku kori PDP da APC a 2023

  • Gabanin zaben 2023, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, Peter Obi ya aike da wani muhimmin sako ga matasan Najeriya da mata 'yan kasuwa
  • Yayin da yake neman goyon bayansu, Obi ya bayyana cewa jam’iyyar APC mai mulki da kuma jam’iyyar adawa ta PDP ba za su yi nasara ba a babban zabe mai zuwa
  • Tsohon jigon na PDP ya lura da cewa zai yi takara ne don amfanin matasa masu tasowa da ’yan kasa da ba a ma haifa ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ogun - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, a ranar Larabar da ta gabata ya ce jam’iyyar APC mai mulki da PDP ba za su ci zaben 2023 ba, saboda jam’iyyun sun buga kuma sun rasa nasaba da siyasa a kasar nan, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Atiku ya nemi hadin kan Wike, Saraki da sauran jiga-jigan PDP don lallasa APC

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan wata ganawa da shugabanni da mambobin jam’iyyar a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Ku kori APC dda PDP a zaben 2023, inji dan takarar LP
Sako ga matasan Najeriya: Ya rataya a wuyanku ku kori PDP da APC a Najeriya | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Obi, wanda a kwanakin baya ya yi murabus daga babbar jam’iyyar adawa, ya ce PDP ta sauka daga turbar sa'a da nasara bayan ta ki mika tikitin takarar shugaban kasa zuwa yankin Kudu.

Peter Obi ya ragargaji PDP

Da yake magana ta bakin Darakta Janar na yakin neman zabensa, Dakta Doyin Okupe, Obi ya caccaki jam’iyyar PDP da rashin adalci ta hanyar yin watsi da tsarin shiyya-shiyya na jam’iyyar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa, wadanda ke adawa da tsarin shiyya-shiyya a jam’iyyar PDP sun durkusar da wanzuwar ta tare da karya yarjejeniyar shugabannin da suka kafa jam’iyyar, kamar yadda This Day ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dan takarar APC: Abu mai sauki ne na lallasa Atiku a zaben 2023, a bani tikiti kawai

Obi ya ce, yana da nufin dawo da martabar ma'aikata a Najeriya kan turba inda ya ce matasa, da kuma mata 'yan kasuwa ya rataya a wuyansu su kori APC da PDP a babban zaben 2023.

A cewarsa:

“Jam’iyyar Labour a cikin shiri har yanzu karamar jam’iyya ce, amma ba wai ba mu san da hakan bane kafin mu dawo nan. Amma jam'iyyar Labour babba ce da ke barci.
"Tasirin da ake iya samu na jam’iyyar Labour ya fi ninki uku na yawan mambobin APC da PDP. NLC, TUC, NURTW, mata 'yan kasuwa, kungiyoyin wararru, dalibai duk suna cikin jam’iyyar Labour.
“Dabarunmu za su kasance mu farfado da ma’aikatan Najeriya. Najeriya za ta ga abin da ba ta taba gani ba, za a ja wandon APC da PDP har kasa.”

Dan takarar APC: Abu mai sauki ne na lallasa Atiku a zaben 2023, a bani tikiti kawai

Kara karanta wannan

Ba zan yi amai na lashe ba: Martanin gwamna Wike da ya sha kaye bayan ganawa da Atiku

A wani labarin, wani rahoton Punch ya ce, Fasto Tunde Bakare, ya bayyana kwarin gwiwar ganin ya kayar da dan takarar shugaban kasa na PDP, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, idan har aka ba shi tikitin jam’iyyar APC.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai, dan takarar shugaban kasar ya bayyana gamsuwa da tsarin tantancewar da APC ta gudanar.

Ya bayyana dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya cancanta a a matsayin abokin gwabzawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel