Sarkin Bauchi ya yi maza ya yi karin-haske, ya karyata jita-jitar goyon bayan Osinbajo

Sarkin Bauchi ya yi maza ya yi karin-haske, ya karyata jita-jitar goyon bayan Osinbajo

  • Sarkin Bauchi ya fitar da sanarwa ta musamman bayan ziyarar da Yemi Osinbajo ya kawo masa
  • Hakan ya zama dole bayan an fara rade-radin Alhaji Rilwan Suleiman Adamu yana tare da Osinbajo
  • Mai martaba ya bayyana ainihin abin da ya faru da Mataimakin shugaban kasa ya ziyarci fadarsa

Bauchi - Mai martaba Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwan Suleiman Adamu, ya karyata rahotannin cewa ya yi mubaya’a ga Farfesa Yemi Osinbajo a zaben 2023.

A wata takarda da majalisar Sarkin ta aikawa ‘yan jarida, wanda ya shigo hannun Legit.ng, Rilwan Suleiman Adamu ya ce ba ya cusa kansa a siyasa.

Wannan takarda ta fito ne a ranar Laraba, 11 ga watan Mayu 2022, daga Babangida Hassan Jahun, wanda shi ne jami’in watsa labarai na masarautar Bauchi.

PM News ta ce masarautar ta yi karin-haske da cewa labaran da ke yawo a gari ba gaskiya ba ne, an kirkire su ne da nufin kawo rashin zaman lafiya a kasa.

Kara karanta wannan

'Batanci: Bayan Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Deborah a Sokoto, Osinbajo Ya Yi Magana Da Kakkausar Murya

Babangida Jahun ya ce abin da ya faru da Mataimakin shugaban kasar ya ziyarci fadar, shi ne Sarki ya fada masa tsoma baki a siyasa ba aikinsu ba ne.

A matasayinsa na Uba, Rilwan Suleiman Adamu ya ce nauyin da ke kansu shi ne bada shawara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sarkin Bauchi da Osinbajo
Jawabin masarautar Bauchi a kan Osinbajo Hoto: pmnewsnigeria.com/Laolu Akande
Asali: UGC

Me Sarki ya fadawa Osinbajo

“Ina so in yi maka maraba da zuwa jihar Bauchi. Na yi imani ka zo Bauchi domin harkokin siyasa ne, amma ka ga bukatar kawo mana ziyara duk da haka.”
“Wannan ya nuna irin kauna da kuma darajar da ka ba masarautar gargajiya.”
“Mun yarda cewa mulki yana hannun Ubangiji, shi ne yake bada shi ga wanda ya so. Haka zalika, mu ba ‘yan siyasa ba ne, na mu shi ne bada shawara.”
“Mu na addu’a ka samu nasara wajen yin duk abin da ya kawo ka Bauchi a yau. Duk abin da zai kawo hadin-kai da zaman lafiya shi mu ke goyon-baya.”

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

Ba a san sarakunan gargajiya da shiga harkar siyasa ba, don haka a al’ada ba su nuna fifiko a siyasa. An san su ne da bada shawarwari idan ana bukata.

Osinbajo ya ziyarci Sarkin Gombe

A makon nan ku ji labari cewa Mataimakin shugaban kasa watau Farfesa Yemi Osinbajo ya je Gombe domin samun kuri’un ‘ya 'yan APC a zaben fitar da gwani.

Da ya ziyarci Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar ya yabi Osinbajo saboda irin halayen kirki da kan-kan da kansa, ya ce abin ayi koyi da shi ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel