Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

  • Kungiyar ASUU ta ce babu abin da zai sa ta janye yajin-aiki sai gwamnati ta cika duk sharudanta
  • An yi zama da malaman jami’ar a fadar Aso Rock Villa da nufin ganin an bude jami’o’in Najeriya
  • A karshe zaman bai haifar da ‘da mai ido ba, shugaban ASUU ya ce za su cigaba da yajin-aikin na su

Abuja - Kungiyar ASUU ta malaman jami’a ta yi watsi da rokon da aka yi mata na cewa ta janye yajin-aiki domin daliban jami’a su koma bakin karatunsu.

Rahoton da Daily Trust ta fitar a ranar Alhamis, 13 ga watan Mayu 2022, ya bayyana cewa shugabannin kungiyar ASUU sun hakikance a kan bakarsu.

Malaman jami’ar sun bayyana wannan matsaya ne bayan sun tashi zaman da suka yi da jami’an gwamnati a fadar Shugaban kasa na Aso Villa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa Buhari ba zai binciki wadanda ke siyan fom din miliyan N100 ba

Farfesa Ibrahim Gambari a matsayinsa na shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ya gayyaci kungiyar malaman jami’a domin a tattauna kan yajin-aikin.

Chris Ngige ya halarci zama da ASUU

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi na kasa, Sanata Chris Ngige ya samu damar halartar wannan taro da aka tashi ba tare da an cin ma matsaya ba.

Farfesa Emmanuel Osodeke wanda shi ne shugaban kungiyar na kasa, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta daina biyansu albashinsu tun kwanaki.

ASUU ta cigaba da yajin-aiki
Dalibar Jami'ar Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

An rahoto Osodeke yana cewa gwamnati tayi wannan ne da nufin tursasa malaman su koma aiki.

Za mu cigaba da yajin-aiki - ASUU

Shugaban kungiyar na ASUU, ya jaddada cewa za su cigaba da yajin-aikin da su ke yi har sai gwamnatin Najeriya ta biya masu bukatun da suka gabatar.

Kara karanta wannan

Ciwon zuciya zai kama wasu: Gwamnan CBN ya ce burinsa na gaje Buhari na bashi dariya

Koke-koken ASUU sun hada da: biyan kudin gyara jami’o’i da hana malamai alawus da kudin karin matsayi, da kuma neman amfani da manhajar UTAS.

Haka zalika kungiyar na so gwamnati ta cika duba yarjejeniyar da aka yi a 2009 da aka gaza cikawa. Shekaru fiye da goma kenan ana faman dauki ba dadi.

Kafin ayi wannan zama, an ji Mai girma Muhammadu Buhari ya roki malaman jami’an su yi hakuri su dakata da yajin-aikin da aka soma tun farkon bana.

Tun a karshen shekarar da ta wuce aka ji kungiyar ASUU ta malaman jami’a ta na gargadi cewa muddin aka garkame jami’o’in, to sai lokacin da Allah ya yi.

A wani taron manema labarai da ASUU ta kira a jami’ar Nnamdi Azikiwe, Awka, jihar Anambra, ASUU ta ce babu ranar dawowa idan aka bari aka rufe jami'o'i.

Asali: Legit.ng

Online view pixel