Sauya sheka: Gwamna Ayade zai san makomarsa ranar Juma'a a rikicin da ake don ya koma APC

Sauya sheka: Gwamna Ayade zai san makomarsa ranar Juma'a a rikicin da ake don ya koma APC

  • Gwamnan jihar Cross Rivers, Ben Ayade, zai san makomarsa a ranar Juma'a a rikicin da ake don ya koma APC
  • Jam'iyyar PDP ce ta shigar da kara gaban babbar kotun tarayya ta Abuja, ta nemi a kwato mata kujerarta da Ayade ya tsere da shi zuwa APC mai mulki
  • Mai shari'a Taiwo Taiwo wanda ya tsige yan majalisar dokokin jihar 20 shine zai kuma zartar da hukunci kan shari'ar Ayade da mataimakinsa

Abuja - Babbar kotun tarayya da ke Abuja za ta yanke hukunci kan karar da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta shigar kan Gwamna Ben Ayade na jihar Cross River, a ranar Juma’a, 25 ga watan Maris, rahoton The Nation.

Jam’iyyar PDP ta hannun lauyanta, Emmanuel Ukala, SAN, ta shigar da wata kara mai lamba: FHC/ABJ/CS/975/2021 a gaban mai shari’a Taiwo Taiwo inda ta nemi a tsige gwamnan da mataimakinsa kan sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Kotu ta kwace kujerun wasu yan majalisa 20 saboda komawa APC

Sauya sheka: Gwamna Ayade zai san makomarsa ranar Juma'a a rikicin da ake don ya koma APC
Gwamna Ayade zai san makomarsa ranar Juma'a a rikicin da ake don ya koma APC Hoto: The Nation
Asali: UGC

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN), ta tattaro a ranar Talata, daga kotu ta 7, inda Mai shari’a Taiwo ke jagoranci cewa za a zartar da hukunci da jam’iyyar PDP ta shigar kan gwamnan Cross River da mataimakinsa a ranar Juma’a mai zuwa.

An dai shigar da karar gwamnan, mataimakinsa da yan majalisa ne a tare, amma tuni kotu ta zartar da hukunci kan mambobin majalisar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Idan za ku tuna, Legit Hausa ta kawo a baya cewa kotu ta sallami wasu mambobin majalisar dokokin jihar Cross River su 20 a ranar Litinin, 21 ga watan Maris.

Mai shari’a Taiwo ya yanke, ya riki cewa ya zama dole yan majalisar su sauka daga kujerunsu kasancewar sun yi watsi da jam’iyyar da ta dauki nauyin kawo su kan mulki.

Vanguard ta kuma rahoto cewa alkalin ya bayyana cewa abun damuwa ne yadda yan siyasa a kasar suke daukar al’umman kasar kamar basu da wani amfani da zaran sun dare kan kujerar mulki.

Kara karanta wannan

Shugabar APC ta mutu a wajen musayar wuta tsakanin ‘Yan bindiga da ‘Yan banga

Ya ce:

“Dole wata rana za ta zo lokacin da zababbun jami’ai za su yi murabus daga kujerarsu ko kuma mutane su tambayi mutanen da suka zabe su kafin su sauya sheka zuwa sauran jam’iyyun siyasa, maimakon sauya sheka zuwa wata jam’iyya ba tare da komawa ga doka ko yan kasar ba.”

A cewarsa, ba zai yiwu mu ci gaba da aikata zunubi ba sannan mu sa ran ganin alkhairi ba.

Yan sanda sun karbe majalisar Cross River bayan tsige yan majalisa 20

A gefe guda, jaridar Daily Trust ta rahoto cewa sashi daban-daban na rundunar yan sandan Najeriya sun karbe dukka hanyoyin da ke sada mutum ga harabar majalisar dokokin jihar Cross River.

Sun mamaye wuraren ne tun da misalin karfe 6:00 na asubahi kamar yadda shaidu suka bayyana.

Sashin yan sandan da ke kasa sun hada da na yaki da garkuwa da mutane, masu yaki da kungiyar asiri da kuma jami’an yan sanda na yau da kullum, dukkansu dauke da makamai.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Kotu ta ba da umarnin soke batun hana APC taron gangamin ranar 26 ga Maris

Asali: Legit.ng

Online view pixel