Shugabar APC ta mutu a wajen musayar wuta tsakanin ‘Yan bindiga da ‘Yan banga

Shugabar APC ta mutu a wajen musayar wuta tsakanin ‘Yan bindiga da ‘Yan banga

  • Kwanakin baya ne ‘Yan bindiga suka yi garkuwa da wasu shugabannin jam’iyyar APC a Kwara
  • Daga ciki har da wasu jagorori na mata na APC a wasu mazabu wanda yanzu haka ta rasa ranta
  • Olomi Sunday ta cika ne a yayin da ‘Yan banga suke musayar wuta da wadannan miyagun mutane

Kwara - Wata shugabar mata a jam’iyyar APC a yankin Koro, karamar hukumar Ekiti, jihar Kwara ta gamu da ajalinta a hannun ‘yan bindigan da suka sace ta.

Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Lahadi, 20 ga watan Maris 2022 cewa Olomi Sunday ta mutu ne yayin da wasu ‘yan sa-kai ke kokarin kubutar da ita a jiya.

Wannan Baiwar Allah ta na cikin shugabannin mata na jam’iyyar APC uku da aka yi garkuwa da su a hanyarsu ta dawowa daga wajen wani taron jam’iyya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai sabon hari Zamfara, sun sheke dagacin kauye da wasu mutum 19

Jaridar ta ce an gudanar da taron rantsar da shugabannin jam’iyyar APC mai mulki da aka zaba ne a gidan gwamnatin jihar Kwara a wancan makon da ya wuce.

Baya ga wadannan mata, an kuma dauke wasu maza uku a wata mota da ta fito daga jihar Ekiti. ‘Yan bindigan sun bukaci a biya N20m a matsayin kudin fansa.

Gwamna AbdulRazaq
Gwamnan Kwara, Abdulrahman AbdulRazaq Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Alasi da Oloke sun sha

Sauran matan da aka dauke su ne Reachel Alasi (shugabar mata ta mazabar Obbo Ayegunle) da takwararta, Yemisi Oloke Oni (shugabar mata ta mazabar Eruku).

Ita Olomi Sunday ce ta rasa ran ta a yayin da ake barin wuta tsakanin wadannan miyagu da suka dauke su da kuma ‘yan bangan da su ke kokarin kubutar da su.

Kamar yadda mu ka samu rahoto daga wata majiya, an tara wannan kudi har N20m za a biya ‘yan bindigan, amma ‘yan banga na sa-kai suka ce za su iya ceto su.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Kotu ta ba da umarnin soke batun hana APC taron gangamin ranar 26 ga Maris

Wannan ya jawo aka yi ta zuba barin wuta a ranar Lahadi, a haka ne aka rasa Olomi Sunday.

Wasu sun samu rauni

Sauran duk sun kubuta, a cikin mazan da aka dauke akwai wadanda suka samu rauni a harin. Sai da na su bai yi muni sosai ba, mutum guda ne ke jinya a asibiti.

Wani ‘dan siyasa a jihar Kwara, Hon Ganiyu Gabriel Afolarin ya tabbatarwa manema labarai cewa shugabar mata ta APC ta mazabar Eruku ta cika a ranar Lahadi.

Saliu Atawodi v EFCC

Ku na sa labari cewa tun 2015 ake zargin VM Saliu Atawodi (rtd) da hannu a badakalar N600m na kudin makamai, sai yanzu aka kammala shari’a a kotun Abuja.

A makon jiya Alkalin babban kotun tarayya, Emeka Chikere ya amince EFCC ta karbe dukiyar tsohon sojan da mai dakinsa, a maida asusun gwamnatin kasa.

Kara karanta wannan

Babu shiri, dole Shugaban PDP ya tada taro saboda za a kawo tashin hankali kan tutar 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel