Da dumi-dumi: Kotu ta ba da umarnin soke batun hana APC taron gangamin ranar 26 ga Maris

Da dumi-dumi: Kotu ta ba da umarnin soke batun hana APC taron gangamin ranar 26 ga Maris

  • Damar gudanar da taron gangamin jam'iyyar APC) na kasa kamar yadda aka tsara a yanzu yana nan daram
  • Wata babbar kotun birnin tarayya ta yanke hukunci a ranar Juma’a, 18 ga watan Maris, ta kori umarnin hana jam’iyyar gudanar da taronta na gangami
  • Wani dan jam’iyyar APC, Hon. Salisu Umoru, shi ne ya shigar da APC kara tare da neman a soke gudanar taron a ranar 26 ga watan Maris

Abuja - Wata babbar kotu a babban birnin tarayya Abuja ta bayar da umarnin soke batun hana taron jam’iyyar APC na ranar 26 ga Maris, Daily Trust ta ruwaito.

Mai shari’a Bello Kawu a yau Juma’a ya bayyana cewa mamban jam’iyya bai da ikon kai karar jam’iyya gaban kotu.

Kotu ta nemi soke batun hana APC taron gangami
Da dumi-dumi: Kotu ta ba da umarnin soke batun hana APC taron gangami ranar 26 ga Maris | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ya ce hukuncin da aka yanke a ranar 18 ga watan Nuwamba, 2021, ya ci karo da hukuncin da kotun koli ta yanke kwanan nan kan wani lamari makamancin haka.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kotu ta umarci AGF ya cire sashen da Buhari ya nema a cire daga dokar zabe

Kotu ta sanya ranar 30 ga Maris don gabatar da cikakken kara, kamar yadda TheCable ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An tattaro cewa wani dan jam’iyyar APC, Hon. Salisu Umoru, ya nemi a hana jam’iyyar APC, Gwamna Buni da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) gudanar da duk wani taro har sai an yanke hukunci.

Rikicin APC: Abubuwan da Gwamna Buni da Bello suka tattauna a ganawarsu

A wani labarin, Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja a ranar Juma'a ya ziyarci takwaransa na jihar Yobe, Mai Mala Buni, kuma shugaban kwamitin riko na jam'iyyar APC na kasa (CECPC).

Idan baku manta ba, rahoton jaridar Tribune ya bayyana cewa, gwamna Buni da Bello sun shiga ganawa bayan dawowar Buni.

A cikin wata sanarwa da babban daraktan yada labarai na Buni, Alhaji Mamman Mohammed ya fitar a Damaturu, ya ce Bello ya jagoranci sauran mambobin tawagar CECPC wajen tarbar Buni a dawowarsa gida daga jinyar da ya yi a Dubai, PM News ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kungiyar Izala ta rabawa yan gudun Hijra da matsalar tsaro ta shafa a Neja kayayayyki

Asali: Legit.ng

Online view pixel