Da dumi-dumi: Kotu ta kwace kujerun wasu yan majalisa 20 saboda komawa APC

Da dumi-dumi: Kotu ta kwace kujerun wasu yan majalisa 20 saboda komawa APC

  • Alkalin babbar kotun tarayya da ke Abuja ya fatattaki wasu yan majalisar dokokin jihar Cross River su 20 daga kan kujerunsu
  • An tsige yan majalisar ne saboda sun sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC
  • Mai shari'a Taiwo Taiwo ya zartar da hukuncin ne a ranar Litinin, 21 ga watan Maris bayan wata kara da jam'iyyar adawa ta shigar

Cross River - Babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja, ta sallami wasu mambobin majalisar dokokin jihar Cross River su 20 a ranar Litinin, 21 ga watan Maris.

Kotu ta kwace kujerun su ne saboda sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam’iyyar All Progressive Congress (APC) mai mulki.

Da dumi-dumi: Kotu ta kwace kujerun wasu yan majalisa 20 saboda komawa APC
Da dumi-dumi: Kotu ta kwace kujerun wasu yan majalisa 20 saboda komawa APC
Asali: Original

Kotun, a wani hukunci da mai shari’a Taiwo Taiwo ya yanke, ya riki cewa ya zama dole yan majalisar su sauka daga kujerunsu kasancewar sun yi watsi da jam’iyyar da ta dauki nauyin kawo su kan mulki.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Kotu ta yanke hukunci kan Bukatar Gwamna Umami da ta tsige kan komawa APC

Jaridar The Sun ta rahoto cewa hukuncin ya biyo bayan wata kara mai lamba FHC/ABJ/CS/975/2021, da PDP ta shigar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kotu ta yi watsi da bukatar gwamna Umahi da aka kwace kujerarsa

A wani labari na daban, babbar Kotun tarayya dake Abuja ta yi watsi da bukatar gwamnan Ebonyi, Dave Umahi, mataimakinsa da yan majalisu 16 na tsayar da batun sauke su daga kan mulki.

Daily Trust ta rahoto cewa Alkalin Kotun, Mai Shari'a, Inyang Ekwo, shi ne ya yanke hukunci bayan masu ƙara sun janye bukatarsu.

The Nation ta rahoto Alƙalin ya ce: "Bayan samun bayanan ɗaukaka ƙara, da kuma bukatar janye batun dakatar da zartar da hukunci daga masu ƙara, Kotu ta yi watsi da lamarin."

Asali: Legit.ng

Online view pixel