Muna Da Hujja Da Ke Nuna PDP Ce Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa a 2019, in Ji Ayu

Muna Da Hujja Da Ke Nuna PDP Ce Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa a 2019, in Ji Ayu

  • Babban jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP, ta yi ikirarin cewa tana da hujja da ke nuna ita ta lashe zaben shugaban kasa a shekarar 2019
  • Dr Iyorchia Ayu, shugaban jam'iyyar PDP na kasa ne ya bayyana hakan, a ranar Alhamis yayin ganawarsa da tawagar masu saka ido kan zabe na EU
  • Shugaban na PDP ya kuma yi alfaharin cewa cikin shekaru 16 da jam'iyyarsu ta yi mulki a Najeriya ta tsare demokradiyya tare da gina hukumomi da za su karfafa ta

FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, na kasa, Dr Iyorchia Ayu, a ranar Alhamis ya ce jam'iyyarsu ne ta lashe zaben shugaban kasa ta shekarar 2019.

Ya kuma ce demokradiyya tana cigaba da tabarbarewa a Najeriya cikin shekaru bakwai da suka shude a karkashin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari: Zaben 2023 zai fi kowane zabe zama sahihi saboda kokarin Buhari

Muna Da Huja Da Ke Nuna PDP Ce Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa a 2019, in Ji Ayu
Shugaban PDP, Ayu: Muna Da Huja Da Ke Nuna Jam'iyyar Mu Ce Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa a 2019. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Ayu ya yi wannan jawabin ne yayin da ya tarbi wata tawagan mutum bakwai ta Masu sanya ido kan zabe na Tarayyar Turai, karkashin jagorancin babban mai sa ido kan zabe, Maria Arena.

Ba za mu dena magana ba har sai an gyara matsalolin Najeriya, Ayu

A cewar wata sanarwa mai dauke da sa hannun mashawarcinsa na musamman kan sadarwa da tsare-tsare, Simon Imobo-Tswam, Ayu ya shaida wa tawagar da EU cewa rahotonta na babban zaben 2019 ya haska wasu daga cikin matsalolin yana mai cewa 'za mu cigaba da magana idan aka cigaba da yin abubuwan da suka saba wa demokradiyya.'

Mu muka ci zaben shugaban kasa na 2019 amma ba a yi mana adalci ba, Ayu

Ya ce:

Kara karanta wannan

Da duminsa: Gwamnatin tarayya ta amince a mikawa Amurka Abba Kyari

"Mun yi imanin cewa mu ne muka lashe zaben shugaban kasa na shekarar 2019. Muna da hujja. Amma ba a yi adalci ba.
"Yanzu muna fuskantar wata zaben a shekarar 2023, yana da muhimmanci mu jadada bukatar da ke akwai na hukumar zabe ta zama mai zaman kanta a hakika."

Ya yi alfahari da cewa jam'iyyar PDP, cikin shekaru 16 da ta yi kan mulki ta tsare demokradiyyar Najeriya ta kuma gina hukumomi da za su karfafa demokradiyyar.

A cewarsa, jam'iyyar PDP ta yi imani da demokradiyya.

2023: Za mu bi didigin inda ƴan takara suke samo kuɗi, za mu sa ido kan asusun bankin ƴan siyasa, INEC

A wani rahoton kun ji cewa Hukumar zabe mai zaman kanta na Najeriya, INEC, ta aika da muhimmin sako ga yan siyasa da jam'iyyun siyasa gabanin babban zaben shekarar 2023.

Hukumar ta sha alwashin cewa za ta saka idanu a kan 'yan siyasa da jam'iyyun siyasa domin gano inda suke samo kudade domin yakin neman zabe, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Dattawan Arewa Sunyi Taro, Sun Yanke Shawarar Goyon Bayan Igbo Ya Maye Gurbin Buhari

Shugaban INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya bayyana hakan yayin wani taro da hukumar zaben ta shirya a Abuja, ranar Juma'a 21 ga watan Janairu, kuma ya ce hukumar za ta saka ido kan yadda aka hada-hadar kudade ranar zabe don dakile siyan kuri'u, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel